MAKAMASHI: Nasara ba ta ga rago

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Wannan ƙasa ta Najeriya, Allah maɗaukakin sarki ya albarkaceta da dukkan wani sunadari na gina duniya, da farko ya bata al’umma sama da Miliyan ɗari biyu da hamsin, ta na kan gaba a ɗaukacin Nahiyar Afrika.  A faɗin ƙasa ta na da murabba’in kilomita 923, 773 wannan abin alfahari ne, domin kuwa tafi dukkan sauran ƙasashen yammacin turai da muke ta kokawar kwaikwayon su.

Ta fuskar yanayi na muhalli, Najeriya ba ta san aman wutar dutse ba, bata san girgizar ƙasa ba, haka ba tasan gocewar ƙasa ba, bata san guguwa daga teku ba, balantana wutar daji. Baya ga haka Najeriya bata san ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ba, kamar yadda muke ji a wasu gurare a Nahiyoyin duniya. Ƙasar noma kuwa Najeriya Allah ya albarkace ta da yanayi na turɓaya da za’a shuka duk wani haki da ɗan Adam, da dabbobi da kuma tsintsaye zasu ci su rayu.

Idan muka koma sha’anin albarkatun ƙasa musamman ma’adanai da kuma makamashin wuta Najeriya babu kamarta a duk faɗin Afrika domin ta na da gwal, man fetur da gas da hasken rana na sama da awa goma sha biyu. Ga kuma iska da take kaɗawa na tsahon wata shida daga kudu zuwa yamma, su ake kira watanni damina a Najeriya, akwai kuma iska mai ƙadawa daga Arewa zuwa gabas, watan da ake kira watannin Kaka da kuma Rani, watannin bushi, abinci da ciyar da Afrika baki ɗaya, ko da kuwa basa noma.

Bincike na kwakwaf, ya nuna cewa ‘yan Najeriya sama da shekaru dubu uku da ɗari bakwai kafin haihuwar Annabi Isa (A.S), wato (3,700 BC) suke da fasaha da kimiya da fasaha na binciko ma’adanai kamar tama da tagulla da zinare da azurfa da bakin ƙarfe da kuma sauran duwatsu na alfarma. Saboda ba zuwan turawa bane, ko kuma ba turawa bane suka nuna musu sanin ƙarfe da kuma amfanin dashi.

Domin akwai ƙabilun NOK na jihar Plateau a yankin Naragata kusa da Jos, ga Dala da Gaya da Ruruwe a Jihar Kano, Mutanan Tarug, kusa da Abuja bincike ya nuna cewa sama da shekara ɗari biyar kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) suke sarrafa tagulla. Mutanan yankin Benin suna sarrafa Bakin ƙarfe da tagulla da Azurfa ta hanyoyi daban-daban har sun ƙware wajan gina gumakan sarakunan su da shahararrun mutanen da sukayi fice a cikin su.

Wannan nasara da aka samu ta faru ne saboda ƙwazo da dagewa da kuma kishin neman na kai, wannan kuwa sai ya samar da al’umma jajirtaciya, kuma tsayayya mai buri da manufa a rayuwa. Ta haka ne masana’antu suka bijiro da farko manoma, makiyaya, maƙera, masu sana’ar binciken ma’adanai (minerals eɗploration) masassaƙa, maɗinka, yan kasuwa da dilallai har ma da masu bayar da ɗinshadi a cikin al’umma (entertainers), wato makaɗa da mawaka da kuma masu wasan barkwanci.

Duk wannan ba zai samu ba da ragwantaka, wato ba hali ne na ragwaye, wato malalata, ana buƙatar jarimai, managartan mutane idan sukace, basa ci’a domin haka, idan suka ce a’a. daɗin baki baya sa su su sauya. Hakan ta kai da samar da garuruwa da suka shahara, misali anan arewa muna da Kano, Katsina, Daura, Yola, Maiduguri, Sokoto, Birnin Kebbi, Mini dukkan su sai da labarin su ya kai tekun maditireniya a Arewacin Afrika, a kudu kuwa labarin su ya kai ƙahon Afrika ha rma yak eta tekun Baharmaliya. Ansan waɗannan ƙasashe a kurmi na ƙasar Gwanja da Gwalkwast da cikin Tekun Atalantika. A ƙasashen yamma shiyasa ƙabilun wangarawa daga Mali da Morokko suka zo ƙasar Hausa.

Mutane suna tambaya daga wane lokaci mutanan Najeriya suka zama cima zaune domin anga irin rawar da suka taka wajan hanyoyin mota da hanyoyin jiragen ƙasa, lokacin da Turawa ‘yan mulkin mallaka da suke kwasar amfani gona da fatu da kiraga daga nan Arewa da kuma katako da kuma ƙwarar manja zuwa ƙasar Ingila da Faransa da Potugal. Haka da suka juyo kwasar ma’adanai zuwa masana’antu su, hazakaƙan ‘yan Najeriya su suka yi aikin TILAS, domin a lokacin aikin hakuma tillas ne “aiki ne na mari da kuma tsinka jaka”.

Daga 1953 lokacin da makamashin man fetur da gas da kuma dangogin sa suka fito kuma suka fara kudi a wannan ƙasa. Har ta kai ga a 1975 Najeriya ta zama itace ƙasa ta bakwai a duniya a wajen samar da man fetur. Tana samun kuɗi har naira Miliyan 3,122 idan aka kwatanta da naira Miliyan 368 wanda ta samu a 1965. Wannan yasa Yakubu Gowon da yake mulki da kansa yayi ikirarin cewa, “kudi basu ne matsalar Najeriya ba, yadda za’a kashe kudin”.

A watan Afrilu na shekara ta 1974, kwamishin saka nazarin albashi na ƙasa, cif udoji, yayi bonus ga ‘yan ƙasa ta ƙasa ladar ƙwadago kuma ya ruɓanya fensho, har aka riƙa ba kowanne dan ƙasa kyautar kudi koda kuwa ba ma’aikatan gwamnati bane. Daga wannan lokaci ‘yan Najeriya suka faɗa kasuwa wajan sayen kayan alatu Keke, Babur, Motoci, Talbijin, Radiyo, Kayan Kade-Kade da kayen bushe-bushe aka koma cin cakulet da biskit, samari da ‘yan mata suka tuba da cin tuwon dawa ko gero aka koma, har ta kai babu sunan da ba a gayawa tuwo.

Daga wannan lokaci aka fara samun ɓarayin zaune da ɓarayin biro har ta kai aka samar da masu ɗaukar makami. Kafin kiftawa da bismillah sai hauhawar farashi ya kunno kasuwa, cin hanci da rashawa suka samu gindin zama. Wannan ya sa shuganni tun daga Murtala Muhammad, Obasanjo, Shagari, Muhammad Buhari, Ibrahim Babangida, Cif Ernest Shonekan, Janar Sani Abacha, da kuma janar Abdussalamu Abubakar, babu wanda baiyo nasa ƙoƙarin ba domin dawo da ‘yan Najeriya kan turba, amma abubuwa sunki zama daidai,

Shekara ta 1999 zuwa yau, 2024 shekaru ne na gwada tsarin dimokaraɗiyya, tsarin da yazo da ‘subsidy’ da sunan tallafin ilimi, tallafin hanyo, tallafin addinai domin yin addu’o’I na zaman lafiya a ƙasa, kai take babu abin da bashi da tallafi a Najeriya, idan ana so aba wasu rukunin Jama’a kuɗaɗe daga gwamnati sai a kira su da tallafi. Saboda haka cire tallafin man fetur da dangogin say a haifar da faɗawa rijiya gaba dubu. Fitowa daga wannan rijiya ba aiki ba ne na rago, domin ragwanci baya kaiwa ga nasara.

By ukarofi