Wani ɗan sanda da ke cikin maye ya harbe mahaifinsa a Borno

Spread the love

Wani ɗan sanda ya harbe mahaifinsa, ASP Wadzani Ntasiri, wanda ya kasance mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) mai ritaya, bayan wani saɓani da su ka yi ranar Lahadi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Sajan ɗan sandan wanda aka bayyana sunansa da Linus Wadzani, ma’aikacin tsaro ne a harabar majalisar dokokin jihar Borno.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar da ke Maiduguri, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), ASP Nahum Daso, ya ce mahaifin ɗan sandan da ya kashe shi ya yi aiki da rundunar ‘yan sandan jihar kafin ya yi ritaya.

Da yake ba da labarin lamarin, PPRO ya ce Sgt Linus ya isa gida da misalin karfe 4:30 na yamma kuma sun yi tafka kazamin faɗa da mahaifin wanda ya kai shi harbin mahaifin sau da dama da bindiga ƙirar AK47 wanda ya kai ga mutuwarsa nan take.

A wata ziyara da suka kai gidan marigayi ASP Wadzani Ntasiri da ke unguwar Modugannari a cikin birnin Maiduguri, wani dan uwa ya bayyana cewa lokacin da Sgt Linus ya dawo gida a ranar Lahadin da ta gabata, babu kowa a gida sai mahaifin marigayin don haka babu wanda zai iya bayar da labarin ainihin abin da ya faru.

“An tattara wata tawaga domin yin bincike daga rundunar, kuma an ɗibi samfuran jini na Sgt don yin samfur domin tantance yanayin tunaninsa kafin aikata laifin,” in ji shi.

Hukumar ta PPRO ta gargaɗi jama’a musamman masu sayar da barasa da su guji sayar wa ko wanne ɗan sanda da ke bakin aiki.

By ukarofi