Rundunar ‘Yan sanda ta roƙi mazauna Abuja kar su shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kwamishinan ‘Yan sandan birnin tarayya, Abuja, Bennet Igweh ya roƙi al’ummar jihar kar su shiga zanga-zangar da aka shirya za a yi a watan Agusta kan tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya.

Igweh ya nuna damuwarsa kasancewar ɓata gari ka iya amfani da zanga-zangar wajen tarwatsa sabbin ayyukan cigaba da a ka yi a faɗin jihar.

Kwamishinan, ya bayyana hakan ne a yayin hira da manema labarai a ranar Litinin a lokacin da rundunar ta gurfanar da mutane da dama kan zargin fashi a hedkwatar ofisoshinta da ke birnin.

Ya ce, suna aiki tuƙuru wajen kamo ƴan fashi domin tabbatar da zaman lafiya a Abuja inda har jihohin Kaduna, Kogi, da Nasarawa su ke shiga domin cimma hakan inda a yayin yunƙurin nasu aka rasa rayukan jami’ansu guda uku, yana mai cewa basa fatan sake rasa wani jami’insu.

Igweh ya ƙara da cewa, kar al’umma su bari a lalata nasarorin da ministan Abuja da shugaban ƙasa suka samu na cigaba da aka samu a ɓangaren tituna da sauran ababan more rayuwa a babban birnin.

By Babaji