Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar hukumar raya yankin Arewa maso Yamma
Wanda ya ɗauki nauyin ƙudirin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, ya yaba da amincewa da Ƙudurin, ya ce amincewar shugaban ƙasa za ta samar da hukumar da za ta sa baki a ɓangaren gwamnatin tarayya sannan za ta magance taɓarɓarewar ababen more rayuwa a yankin.
Jibril ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Talata cewa, hukumar za ta rage wahalhalun ababen more rayuwa a yankin da Boko Haram da ‘yan bindiga suka lalata.
Ya cigaba da cewa, “Abin da shugaban ƙasa yayi shi ne nuni da cewa shi shugaba ne da za a amince da shi, dole ne mu yi hakuri da shi, mun san cewa ba a gina birnin Roma a rana ɗaya ba. Mu ci gaba da yi masa addu’a. Wannan shekararsa ce kawai, mu ba shi goyon baya, mu yi watsi da masu son su ɗauke masa hankali,”
