Daga USMAN NASIR KAROFI
Gwamna Dauda Lawal ya jinjinawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da ya sanya hannu a kan ƙudurin ƙirƙirar hukumar ci gaban Arewa maso Yamma
A wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa Gwamnan ya yi matuƙar jinjinawa Shugaban domin yin hakan zai kawo cigaba mara adadi ga yankin.
Ya bayyana cewa, hukumar an ƙirƙire ta domin ayyuka irin su gina tituna, gidaje da kasuwanci da suka rushe a yankin. Ya cigaba da cewa, yin haka tabbas zai kawo sauƙi ga raɗaɗin talauci da ake fama dashi.
Ya jinjina ƙwarai da gaske da wannan yunƙuri na Shugaban ƙasan domin yin hakan zai haɓɓaka harkoki da dama a yankin.
