Tsohon Shugaban ƙaramar Ungoggo, Eng Abdullahi Garba Ramat yayi kira da mutanen gari su rinƙa tuhumar gwamnonin jihohin su kamar yadda suke tuhumar Shugaban ƙasa Tinubu.
Yayi wannan bayanin a shafin sa na dandalin Facebook, inda ya ke cewa tunda a ka cire tallafin mai, yawan kuɗin da jihohi suke samu ya ninka sama da kaso 50, yace ma jihohi irin su Nasarawa, ninki ya kai kaso 100.
Ya faɗa cewa, idan akwai waɗanda ya kamata ayi wa zanga-zanga, gwamnoni ne ba Shugaban ƙasa ba.
Ya cigaba da bada misali ya na cewa, ƙaramar hukuma kamar Ungoggo a watan Yuni, ta samu kuɗin daga Gwamnatin Tarayya kimanin N441,409,733.13, amma ya na da yaƙini Shugaban ƙaramar hukumar bai yi aikin Naira miliyan 50 ba.
Ramat ya bayyana in dai ba mutane sun gane gwamnoni suke hana su cigaba ba, abun kullum ƙara ta’azzara zai yi. Don haka yayi kira da mutane su natsu su gano inda matsalar take.
