Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Alamu sun nuna neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza da ke cikin wata na 9 ya wargaje don yadda hare-haren Isra’ila kan garuruwan na Gaza su ka ƙara ta’azzara. Hamas ta bayyana janyewa daga yarjejeniyar da ƙasar Masar, Ƙatar da Amurka ke jagoranta. Tun fara wannan yaƙi na Gaza a ranar 7 ga watan Oktobar bara ya zama babban lamari da ya ɗauke hankalin duniya kuma a lokaci guda duniyar ta ƙasa dakatar da zubar da jinin fararen hula.
Yanzu ma tamkar a ce ba a ma yaƙin Rasha da Yukrain ko ma na Sudan tsakanin shugaban gwamnatin soja Janar Abdelfatah Burhan da na sojojin sa kai na Janar Hameti Hamdan Daglo. Yaƙin nan na Gaza fa kwantar da labarin damɓarwar Yaman tsakanin zaɓaɓɓiyar gwamnatin birnin Aden na kudanci da ’yan tawayen houthi da ke rike da sassan ƙasar ciki da babban birnin ƙasar San’a’a. Hatta Majalisar Ɗinkin Duniya labarun Gaza ya mamaye ta zuwa ma zaman kwamitin tsaro na majalisar. Hakanan in ka ji a na maganar kotun duniya nan ma batun na Gaza a ke yi amma shiru ba alamun iya tsagaita wuta don ceto sauran mutanen da ke rayuwa zuwa uƙuba da gallazawa a Zirin. Zai yi wuya ka samu ƙasar da za ta juyawa hukuncin kotun duniya baya ko na kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwana lafiya sai Isra’ila. Idan a na bin ta ɓarawo to lalle kuwa a bi ta ma bi sawu don in an duba su kan su Falastinawa sun faɗa cikin rabuwar kawuna inda fadar gwamnatin ƙasar a Ramallah ke ɗaukar ’yan Hamas tamkar wasu ’yan banga har ma gwamnatin ke cewa bayan yaƙin za a tsame hannun Hamas daga mulkin Gaza.
Su ma jagorin Gaza da lalle manyan su dole su ke zaman hijira wa imma a ƙasar Katar ko Lebanon ba sa saurarawa duk wani jagorancin Falasdinawa na Mahmud Abbas. Wato yayin da Hamas ke ganin sai ta hanyar gwagwarmaya za a iya kwato haƙƙin Falastinawa daga mamayar Isra’ila, su kuma hukumomin Ramallah na ganin ta hanyar maganganu da shiga tsakani ne za a iya cimma wannan buri don an shafe shekaru tun 1948 a na ta gwagwarmaya amma ba fa’ida da a ka samu. Hasalima Isra’ila ta cika gidajen yarin ta da Falastinawa dattawa da matasa da ta ke ɗauka na barazana gare ta. Mu tuna irin hikimomi da diflomasiyyar marigayi shuagban Falasdinawa Yasser Arafat amma a ƙarshe haka ya bar duniya ba tare da cimma burin samun ƙasar Falastinu mai ’yanci ba. Lamarin ya zama a zahiri Isra’ila na da uwa a murhu don haka ba wai a na maganar soke ƙasar ba ne amma tamkar a na rarrashin ta ne ta bari a kafa ƙasar Falastinu da ta mamaye a gefen ta su zauna tare a matsayin makwabta. Gaskiya kasashen yamma na marawa Isra’ila baya kuma kullum ba ta laifi a wajen su kuma su kan kauda ido idan ta yi dirar mikiya kan Falasdinawa. Batun tutiyar kare ’yancin ɗan adam ba ya aiki in a na maganar matakan Isra’ila kan Hamas da a ke ɗauka a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba ta gwagwarmayar kare ƙasar Falasɗinu ba. Abun da ke nuna in an matsa lamba ga Falasdinawa za su iya haɗa kai shi ne yanda ba sa kasa a guiwa don mutuwa. Za ka ga an kashewa iyalin Falasdinawa ‘yan uwa amma su na godewa Allah kuma su na yin kamar alfaharin sadaukar da kai ne ga ƙasar su. Harin Isra’ila ya kashe ’ya’ya da jikokin shugaban Hamas Isma’il Haniyeh amma hakan bai sa ya yi ta kururywa ko firgita ba duk da an kai harin ne da gangan don karya ma sa guiwa. Wani abu kuma ina ganin yadda duk wani jami’in Falasdinawa a ketare kama daga ‘yan diflomasiyya ba sa kushe matakan Hamas wato ma’ana su kan nuna zaluncin da a ke yi wa Falastinawa ne ya kawo gwagwarmayar makamai ta Hamas.
Duk yanda ‘yan jarida kan matsawa jami’an don yiwuwar furta wata kalma ta Allah wadai da Hamas ba ya nasara daga bakunan su. Falasɗinawa na faɗan cikin gida ne amma a waje burin su da su ka tsaya a kai shi ne kwato ‘yancin ƙasar su kuma musayar wuta da Isra’ila tamkar martani ne ko kariyar kai ne. A gaba daya za mu iya cewa yayin da Isra’ila ke da manyan makamai da mara baya daga yammacin duniya, su kuma Falasdinawa ba su da makamai sai gwagwarmayar Hamas inda ‘yan uwan su Larabawa kuma ba su da zummar iya kawo mu su ɗauki na kai tsaye sai dai tura agaji da kuma nuna takaici. Siyasar duniya ta sa wasu ƙasashen Larabawa na ƙulla jakadanci da Isra’ila da kuma nuna sassaucin martani kan yadda Isra’ilar ke gallazawa Falasdinawa. Tun yakin da Isra’ila ta yi da ƙasashen Larabawa ta samu nasara a ka samu gagarumin sauyi ta yadda Larabawan ke ɗaukar matakan da za su tserar da ƙasashen su da muradun shugabancin ƙasashen fiye da wani hoɓɓasa da ya shafi dukkan Larabawa.
Ƙungiyar Hamas da ke mulkin Gaza na bukatar a kafa gwamnatin wasu kwararrun da ba su da hannu a kowanne ɓangare ga ƙasar Falasdinu bayan kammala yaƙin Gaza.
Jami’in Hamas Hossam Badran ya bayyana haka a taron masu shiga tsakani na tsagaita wuta a yaƙin Gaza da su ka haɗa da ƙasar Ƙatar, Masar da Amurka.
Badran ya ce sun shaidawa masu shiga tsakanin wannan matsaya ta samun gwamnatin waɗanda ba su da hannu a kowane ɓangare don jagorantar Gaza da kuma yankin yammacin kogin Jodan.
Hakanan Badran ya ce ba za su tattauna da wani a waje da Falastinu ba kan lamuran bayan yaƙin don harka ta cikin gidan Falastinawa.
Kimanin Falasdinawa 90 su ka mutu a sanadiyyar wani mummunan harin da Isra’ila ta kai ta sama kan wani sansanin da Majalisar Cinkin Duniya ke kula da shi a Gaza.
Ƙungiyar Hamas da ke jagorantar Gaza ta bayyana munin harin da wanda ya fi kisan gilla ga Falastinawa a baya-bayan nan.
Isra’ila ta ce harin ya auna shugaban soja ne na Hamas Muhammad Deif da zuwa yanzu ta ke binciken yanayin nasarar harin.
Hamas ta musanta ikirarin na Isra’ila cewa neman shugabannin sojan ta ne da nuna dabarar Isra’ila ce ta samawa harin dalili.
An samu bayanai daga waɗanda su ke da sauran shan ruwa cewa harin ya wargaza bigiren ya kuma daidaita naman jikin mutane har sassan su ka warwatse.
Ƙasar Isra’ila ta dau matakin kai miyagun hare-hare ta sama, ƙasa da ruwa kan Zirin Gaza inda hakan ya yi sanadiyyar asarar rayuka.
Aukuwar hakan ya sanya ƙungiyar Hamas mai mulkin Gaza sanarda janyewar ta daga yarjejenyar tsagaita wuta don musayar kamammu da fursunoni.
Jami’an lafiya a sansanin Al-maghazi sun ce hare-haren sun yi sanadiyyar kashe mutum 5 inda 3 daga cikin su yara ne.
Hare-haren na Isra’ila sun shafi yankin Khan Younis da ma Rafah da ke kudancin Gaza inda mutane a farkon yaƙin na wata 9 su ke samun mafaka.
Wani hari da Isra’ila ta kai Lebanon ya yi sanadiyyar kashe yara ‘yan ƙasar Sham da ke zaman gudun hijira.
Hare-haren na samaniya da Isra’ila ke kai wa garin Ummal Tut a kudancin Lebanon ya karu inda jirgi marar matuƙi ya kashe yaran a yayin da su ke aiki a wata gona kuma a ka ɗauke su a ka yi mu su jana’iza a garin Ƙasimiya.
Rahotanni sun ƙara da baiyana yadda hare-haren na Isra’ila su ka shafi wasu garuruwan kudancin Lebanon da musayar wuta bai daidaita su ba.
Haƙiƙa a na cigaba da gargaɗin musayar hare-hare tsakanin Isra’ila da Hezbollah a Lebanon zai iya faɗaɗa yakin Gaza fiye da yadda a ke ciki a yanzu.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci dakatar da musayar hare-hare da kan shafi kudancin Lebanon da arwacin Isra’ila kuma hare-haren na shafar waɗanda ba ruwan su a fitinar musamman in an duba misalin irin abun da ya faru ga waɗannan yara.
Shugaban Hezbolla Hassan Nasrallah ya nuna damuwa ga abun da ya zayyana yadda abokan gaba wato Isra’ila ke ƙara kai hare-hare kan fararen hula a sassan kudancin Lebanon.
A nan Nasarallah ya ce Hezbollah ta maida martani ta hanyar harba rokoki kimanin 120 kan garin Kiryat Shmona na arewacin Isra’ila ya na mai gargadin in hare-haren su ka cigaba, Hezbollah za ta kai farmaki kan sassan arewacin Isra’ila da ba ta taba ba zuwa yanzu.
Nasrallah ya ƙara da kurarin matuƙar Isra’ila ta nemi mamaye Lebanon a yakin ‘yar gabaɗaya, to za ta wayi gari ba ta da sauran tankuna da za ta yi yaƙi da su.
Kammalawa;
Nauyi ya rataya kan duk masu ruwa da tsaki na duniya su kawo ƙarshen wannan yaƙi da kai wata 9 a na zubar da jinin mata da ƙananan yara a Gaza. Tsawon lokacin da a ka ɗauka a na wannan yaƙi da dubban Falastinawa da a kashe na nuna gazawar duniya kan takawa Isra’ila birki. Duk yunƙurin Isra’ila na gamawa da Hamas ba zai samu nasara ba matuƙar da sauran Falastinawa a Gaza. Kazalika ko an kashe dukkan Gazawa ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ba har dai ba a yi adalcin kafa ƙasar Falasdinu mai cikekken ’yanci da babban birni a gabashin birnin Ƙudus ba.
