INEC za ta iya zaɓukan ƙananan hukumomi a duk faɗin ƙasa – Farfesa Yakubu Mahmud

Spread the love

Makonni biyu bayan da kotun ƙoli ta bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu a Najeriya, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar zaɓen na iya samun nasarar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin idan doka ta ba su dama.

Shugaban na INEC ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki kan harkokin zaɓe domin gabatar da kasafin kuɗin zaɓen Ondo da Edo a ranar Alhamis.

Mahmood ya bayyana cewa, hukumar da a halin yanzu take gudanar da zaɓuka ba tare da tangarda ba a mazaɓu 62 da ke babban birnin tarayya Abuja, babu wani tangarda, hakan na nuni da cewa suma kananan hukumomi 774 da ke faɗin tarayyar za su iya wannan aikin in har doka ta basu dama.

A zaɓen gwamnan Edo da za a yi a ranar 21 ga Satumba, 2024 da kuma zaɓen gwamnan Ondo na ranar 16 ga Nuwamba, 2024, shugaban INEC ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yaba da gagarumin ci gaban fasaha da hukumar ta samu. Ya bayyana cewa yana da yaƙini wannan zaɓen ba za a samu matsalar na’ura ba.

By ukarofi