Burtaniya za ta kashe sama da fan miliyan 10 don aikin mayar da baƙin haure Rwanda

Spread the love

Gwamnatin Burtaniya ta shirya kashe aƙalla Fan biliyan 10 ƙarƙashin sabon tsarin aikin kwashe baƙin haure tare da jibge su a Ƙasar Rwanda kamar yadda ƙasashen biyu suka kulla yarjejeniya.

Sakatariyar harkokin cikin gida ta ƙasar Yɓette Cooper ta ce tuni har an tattara Fan miliyan 700 cikin kuɗin daga hannun masu biyan haraji.

Cooper ta kuma ce waɗannan kuɗaɗe sun haɗa da kuɗin jirgin da zai yi jigilar su, biyan ma’aikatan da zasu sanya idanu wajen ganin an maida su Rwanda, da kuma biyan gwamnatin Rwanda kan wannan aiki da zata yi.

Sabon Prime ministan wasar Keir Starmer wanda ya tarar da wannan tsari da tsohuwar gwamnati ta shimfiɗa ya sha alwashin ɗorawa daga inda aka tsaya, tare da ɗaukar aniyar kai dubban baƙin haure zuwa Rwanda nan da ‘yan watanni.

To sai dai da yake mayar da martani kakakin jam’iyyar Conserɓatiɓe James Cleɓer ya ce wannan kuɗaɗe sun yi yawa a wannan aiki, sannan kuɗaɗen da aka ware don biyan gwamnatin Rwanda cin fuska ne a gareta.

Gwamnatin ƙasar na ci gaba da wannan shirye-shirye ne duk da hukuncin kotun koli na watan Nuwamban bara da ya haramta wannan yunƙuri da ya kira da keta haƙƙin ɗan adam kai tsaye da kuma jefa rayuwar baƙin hauren cikin haɗari.

By ukarofi