Ba ni da iyayen gida da zan sakawa, Inji Tinubu

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kore zargin cewa ya na da waɗanda su ka dafa masa cikin ɗaiɗaikun mutane ko kuma wata ƙungiya a siyasarsa, yayin da ake cigaba da daidaita al’amuran tattalin arziƙi, ya ce shi ya ɗauki nauyin yawon neman zaɓensa ba tare da taimakon wasu mutane ko ƙungiyoyi ba.

Tinubu wanda ya karɓi baƙoncin malaman addinin Islama ƙarƙashin jagorancin Sheikh Bala Lau a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis, ya ce nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa iko ne na Ubangiji da kuma shiri na tsanake tare da samun goyon bayan ƴan Nijeriya.

Shugaba Tinubu ya ce, bai da wani maigida ko waɗansu da su ka ɗauki nauyin al’amuran siyasarsa, yana mai cewa kuɗin da ya kashe a lokacin zaɓe, nasa ne na ƙashin kansa.

A gefe guda, Tinubu ya ce batun zanga-zanga da aka hura wutarta da fushi da tsana, kaɗai ka iya haifar da tarzoma a cikin al’umma tare da mayar da ƙasar baya.

Ya ce, suna cigaba da ƙoƙari wajen ganin an sake samar da hanyoyin bayar da tallafi da alawus ga talakawa da mabuƙata domin rage raɗaɗin halin da ake ciki a faɗin ƙasar.

Haka kuma, za ke bayar da tallafi ga dalibai domin inganta harkokin ilimi da kuma samar da tsarin ‘costumer credit’ da zai bada damar mallakar motoci da gidaje a bashi wanda za a ke biya kaɗan-kaɗan.

Ya kuma ce, sun ƙara mafi ƙarancin albashi da sama da kashi 100, yana mai cewa waɗanda su ka ɗauki nauyin zanga-zangar sun yi hakan ne saboda manufofinsu na son kai ba don al’umma ba.

A lokacin da ya ke jawabi, Bala Lau ya tabbatar da cewa za su cigaba da taimaka wa Tinubu da addu’o’i gami da wayar da kan al’umma, yana mai la’akari da muhimmancin zaman lafiya ga ƙasar da ma al’umma baki ɗaya.

By Babaji