An rufe adireshin ɗaukar ma’aikata a NNPC na wucin-gadi saboda cinkoso

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ruwaito cewa adireshinsa na ɗaukar ma’aikata ya rufe sakamakon cinkoson adadin waɗanda ke shigar da bayanan neman aiki.

NNPC ya buɗe adireshin ne domin cike gurabe daban-daban a ranar Juma’a wanda za a rufe a ranar 20 ga watan Agusta.

Kasancewar masu ziyaratar shafin adireshin sun yawaita, hakan ya sa ya kulle daga karɓar su.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta kafar X, ta ce tawagar jami’an gudanarwa na ƙoƙarin gyara matsalar wacce a ke fatan magance ta nan ba da jimawa ba.

Kazalika, kamfanin ya sake tabbatar wa waɗanda ke ƙoƙarin neman aiki cewa za a bada ayyukan ne bisa ga adalci tare da la’akari da cancanta.

By Babaji