
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Jami’an tsaro ciki har da hedkwatar tsaro (DHQ) da Ƴan sandan farin kaya (DSS) sun ankarar da jami’ansu kan cewa su kasance cikin shiri domin kaucewa tashin-tashina gani yadda lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa na cigaba da ƙaratowa.
Hukumomin tsaron sun bayyana hakan ne ta mabanbanta hanyoyi inda suka tabbatar da cewa ba a yi nufin gudanar da zanga-zangar cikin lumana ba. DSS ta ce, babbar manufar waɗanda ke shirya zanga-zangar ita ce a canza gwamnati a matsayin jigo. DHQ ta ce, wani binciken sirri ya nuna cewa akwai alamun a juya zanga-zangar ta koma rikici.
Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin APC da sarakunan gargajiya tare da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja inda Ribaɗu ya yi kira ga gwamnonin da su taimaka wajen tarar ƙalubalen da zanga-zangar ta ke ɗauke da su.
Ministan Abuja, Nyesom Wike yi ce babu wata zanga-zangar da za a yi a birnin. Haka nan, ƙungiyar kasuwanci ta ƙasa, TUC ta ce ba za ta goyi bayan zanga-zangar da ba ta san waɗanda suka shirya ta ba.
A gefe guda, ƴan majalisar wakilai daga kudu-maso-gabashin Nijeriya sun yi kira ga al’ummarsu ƴan ƙabilar Igbo da su guji zanga-zangar tare da sanar da su cewa ana ƙoƙarin samar da mafita ga matsalolinsu.
