
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Sojoji shida sun rasa rayukansu a lokacin da wani abin fashewa ya tarwatsa wata motar soji a Mungunu da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis inda motar jami’an ta haye kan wani bom ake zargin mayaƙan Boko Haram ne su ka dasa a kan hanyar Gamboru Ngala- Maiduguri, kamar ‘Sahara Reporters’ ta ruwaito.
Rundunar sojin ta samu rahoton cewa, mayaƙan sun kai hari wani gari da ke kusa da inda ta ke.
Jin haka ke da wuya rundunar ta tura motoci uku domin kai mu su ɗauki wanda hakan ya yi sanadiyar aukuwar lamarin inda mutum ɗaya ya tsira a cikin su.
