
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Sufeta Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun ya Umarci duk wata tawaga da ke shirin yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya su bayar da bayanan da ake buƙata ga kwamishinan Ƴan sandan jihar da za a gudanar da ita.
Kayode ya faɗi hakan ne a ranar Juma’a a Abuja inda ya yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da hangen nesa kafin shiga kowace irin zanga-zanga dan gujewa haifar da koma baya wa ƙasa.
Abubuwan da ake buƙatar bayaninsu daga kowace tawaga ta zanga-zangar sun haɗa da;
- * hanyoyin da za a bi da inda za a haɗu yayin zanga-zangar
- * Lokacin da za a ɗauka ana yin zanga-zangar
- * Sunaye da bayanan adireshin shugabannin da masu shiryawa
- * Matakan kariya da za a ɗauka idan aka samu al’amarin sata tare da bayyana waɗanda ake zargin za su iya tayar da rikici
Ya ce matukar aka samar da waɗannan abubuwan, hukumar ‘Yan sanda za ta sanya isassun jami’an tsaro domin bada kariya ga al’umma a yayin zanga-zangar.
Daga ƙarshe, rundunar ta buƙaci al’umma da su bada haɗin kai ga jami’an wajen kiyaye doka da oda domin tabbatar da an yi ta cikin lumana ba tare da cutarwa ba.
