Matatar  Ɗangote: Majalisa ta nemi a gaggauta dakatar da Shugaban NMDPRA

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Wakilai ta bu ƙaci a gaggauta dakatar da Shugaban Hukumar Albarkatun Mai Na  Ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, kan dambarwar hukumar da Matatar Man  Ɗangote.

 Ɗan Majalisar, Esosa Iyawe, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban na NMDPRA har sai majalisar ta kammala bincike kan zargin almundhana da ake wa a hukumar na ba da lasisi ga kamfanonin da ke shigo da man dizel mara inganci Nijeriya daga  ƙasashen waje.

Honorabul Esosa Iyawe ya ce dakatar da shugaban na NMDPRA na da muhimmanci saboda katoɓarar da ya yi, cewa man dizel  ɗin da Matatar  Ɗangote ke samarwa ba shi da inganci idan aka kwatanta da wanda ake shigo da shi daga  ƙasashen waje.

Honorabul Esosa Iyawe ya  ƙara da cewa, “zargin da ake wa NMDPRA na bayar da lasisi ga masu shigo da man dizel mai  ɗauke da sinadarin Sulphur fiye da kima zuwa Nijeriya da kuma amfani da shi a  ƙasar babban ha ɗari ne ga lafiyar al’umma, da kuma asara a ɓangaren tattalin arziki.

“Katoɓarar shugaban na NMDPRA, wanda tuni bincike ya  ƙaryata, ya fusata ’yan Naijeriya, har suna zargin jami’in da yin zagon  ƙasa ga matatun mai na cikin gida.

“Yadda ya dage cewa a ci gaba da shigo da mai daga  ƙasashen waje zangon  ƙasa ne ga tattalin arzikin  ƙasa.

“Sannan gwajin da aka gudanar ya nuna man da ake shigowa da shi na  ɗauke da sinadari (Sulphur) da ke da ha ɗarin gaske fiye da kima,” in ji shi kamar yadda kafar The Nation ta ruwaito.

Ana iya tuna cewa a wata tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban  Ƙasa, Farouk Ahmed, ya yi zargin cewa man dizel  ɗin Matatar  Ɗangote na  ɗauke da sinadarin Sulphur da ya haura 1,200ppm, na  ƙasashen wajen kuma bai haura 650ppm ba.

650 shi ne adadin Sulphur da NMDPRA ta  ƙayyade wa matatun cikin gida a Nijeriya zuwa shekarar 2025, kamar yadda  ƙungiyar ECOWAS ta  ƙayyade da nufin rage fitar da gurɓataccen haya ƙi da kuma kare muhalli.

Sai dai sakamakon gwajin da aka gudanar kan man dizel  ɗin da Matatar  Ɗangote da na  ƙasashen wajen ya nuna ingancin na  Ɗangote sa zarce na  ƙasashen waje nesa ba kusa ba.

Sakamakon gwajin ya nuna Sulphur  ɗin man dizel  ɗin  Ɗangote 87.6ppm ne, a yayin da samfurin na  ƙasashen waje biyu da aka auna ke  ɗauke da 1,8000ppm da kuma 2,000ppm.

Majalisar Wakilai na daga cikin wa ɗanda suka sanya ido a kan binciken da aka gudanar kan samfurin man dizel  ɗin na  Ɗangote da na  ƙasashen waje.

Honorabul Esosa ya ce idan har babban jami’in gwamnati zai yi irin wannan katoɓarar ba tare da bincike ba, akwai alamar rashin  ƙwarewa da kuma rashin kishin  ƙasa, musamman a halin da ake ciki a Nijeriya a halin yanzu.

 Ɗan Majalisar ya ja hankalin abokan aikinsa cewa duk makamashin da ke dauke da Sulphur wanda ke fitar da bakin haya ƙi sosai musamman daga man dizel, yana haddasa cutar kansa da cutar huhu sannan yana lalata injina da kuma gurɓata muhalli.

Shi ya sa  ƙasashen duniya ke  ɗaukar tsauraran matakai don rage adadinsa sosai, ta hanyar yin dokoki da ke wajabta wa masana’antu yin injina da makamashi mai  ƙarancinsa domin kare lafiyar jama’a da kuma muhalli.

By ukarofi