Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fitaccen malamin Musulunci a Nijeriya, Sheikh Tijjani Yusuf Guruntum, ya gwangwaje ɗalibansa da kyautar ku ɗa ɗe da kayan abinci.
Sheikh Tijjani Guruntum ya raba wa ɗaliban nasa wannan kaɓakin arziki ne bayan kammala karatu a ranar Litinin.
Ɗaya daga cikin ɗaliban malamin mai suna Muhammad Sagir Ibrahim, ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna cewa kusan duk ɗaliban da suka halarci majalisin malamin a na ranar Litinin bayan sallar isha’i ya samu wannan kyauta.
Wata majiya ta bayyana cewa malamin ya yi rabon ne ga ɗalibai sama da 50 da suka halarci majalisin.
Rahoton da Manhaja ta samu ya nuna wasu sun samu kwalin taliya da ku ɗi, wasu sun samu ku ɗi Naira dubu 10, wasu kuma dubu 20, wasu kuma 30 har da wa ɗan da suka samu sama da haka.
“Wannan fa zallar [kyautar] ɗalibai ce aka yi yau.
“Za a yi na mutanen gari [daga bi sani] inda aka tanadi shinkafa da gero da sauran kayan abinci da za a raba wa mutanen gari cikin wannan satin in sha Allahu,” a cewar majiyar.
