Daga RABIU SANUSI a Kano
Kwamishinan inganta harkokin karkara na jihar Kano Alhaji Abbas Sani Abbas ya bu ƙaci al’ummar da su sa ido wajen kula da ayyukan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf take gudanarwa da moriyar al’umma dake jihar.
Alhaji Abbas Sani Abbas ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da wakilan gidajen labarai na fadar gwamnatin Kano a ranar Talatar nan.
Kwamishinan ya ce zuwansa wannan ma’aikata akwai abubuwa masu tarin yawa, wanda ya fara da duba yanayin hanyoyin da za su sada mazauna karkara da samun cigaba a fa ɗin jiha.
A.S.A ya ce da sahilewar mai girma gwamna an samar masu da ku ɗin da za su gabatar da gudanar da ayyuka.
“Daga nan mun ƙara tashi tsaye zuwa ma’aikatar ku ɗi ta jiha don a samu a sakar mana ku ɗin da mai girma gwamna ya sahile mana dan fara ayyukan da ya kamata.
Kwamishinan ya ce ya zuwa yanzu sun saki shirye-shiryen gudanar da ayyuka guda 8 guda biyar, hanyoyi sai wasu ayyukan guda 3 don bun ƙasa ayyukan cigaba.
Haka zalika ya ce akwai wasu tituna guda 10 a kananan hukumomi na cikin gari don samun yadda za a cigaba, sai ayyukan gayya don yashe magudanan ruwa na ƙananan hukumomi 8 na cikin gari don kaucewa ambaliyar ruwa.
“Haka kuma akwai hanyoyi guda uku da masu hasashen yanayi don kaucewa wannan ambaliyar ruwa don haka da mun kammala wannan na ƙananan hukumomi 8 ɗin nan na cikin gari.
Ya kuma jaddada shirin ma’aikatar sa na shirin samar da taransfoma don inganta wutar lantarki a kowane lungu da sa ƙo na jihar Kano da za ta kai kimanin guda 500.
Kwamishinan na raya karkara yace akwai yun ƙurin samar da hanya kilomita 500, sai rijiyoyi guda dubu biyar tare da maganar solar don gidajen karkara da basu wuce guda 500 ba da a haska guraren da al’ummar su don inganta rayuwar al’umma.
Abbas sani Abbas ya kuma bu ƙaci al’ummar jihar Kano da su kula da dukkan abinda za a sama masu na cigaban da za su fuskanta don kaucewa ɓatawa da kuma tabbatar ƙarkonsu.
