Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Ƙungiyar Tabbatar da Dimukraɗiyya a Nijeriya, Hon. Abdulrahman Buba Kwacam ya gargaɗi al’ummar Nijeriya da su ƙaurace wa zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu ke ƙoƙarin shiryawa a Nijeriya a farkon watan Agustan nan mai kamawa.
Kwatsam ya bayyana haka ne jiya Alhamis a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja.
Hon. Abdulrahman Buba Kwacan yi kira ga matasa waɗanda za a yi amfani da su domin cimma wata manufa akan ƙorafi na tsadar rayuwa da ke damun al’umma, inda ya ce wasu marasa kishin ƙasa ne ke kawai ke cusa musu ra’ayin yin zanga-zangar.
Ya ce a zahirin gaskiya ba a shirya zanga-zangar don ƙorafi ga gwamnati dangane da tsadar rayuwa da halin da ƙasar ke ci na taɓarɓarewa tsaro ba ne, ya ce abin ba nan ya dosa ba, saboda haka ne suke kira ga al’umma musamman matasa da kada su sake a yi amfani da su wajen yi wa gwamnati ɓarna ko kuma kawo tarnaƙi a cikin ƙasa.
Ya ce masu shirya zanga-zangar suna duba ne da irin ƙasashen Kenya da wasu ƙasashe da suke yin irin wannan zanga-zanga, inda ya ce su suna yi ne domin ci gaban ƙasarsu da al’ummarsu, “amma mu a fahimtarmu wannan zanga-zanga da za a yi ba za a yi ba ne don ci gaban al’ummar Nijeriya, wasu ne suka ƙirƙireta don cimma manufarsu.
“Akwai lauje cikin naɗi a wannan zanga-zanga, wasu ne ke son amfani da ita domin cimma manufarsu.
“Saboda haka muna kira ga matasanmu musamman ‘yan Arewa su ƙaurace wa zanga-zangar da marasa kishin ƙasa ke ƙoƙarin shiryawa domin ɓata ƙasarmu da kuma yankinmu,” inji Kwacam.
