Rikicin matatar Ɗangote: Majalisar Dattijai ta ayyana ranar tattaunawa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Majalisar Dattijai ta zaɓi watan Satumba a matsayin lokacin tattauna batun rikicin da ke tsakanin kamfanin Ɗangote da kuma ofisoshin gudanarwar man fetur da suka haɗa da hukumar NMDPRA da kamfanin NNPC.

Shugaban ƙwarya-ƙwaryar kwamitin da shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya naɗa don sasanci, Sanata Bamidele Opeyemi ya faɗi haka, yana mai cewa za su bayyana dukkan waɗanda ke da hannu cikin kawo rigima a ɓangaren harkar mai a Nijeriya.

Opeyemi ya bada tabbacin cewa kwamitinsu zai samar da sakamako na abin a zo a gani ba kamar irin na kwamitocin da aka yi a baya ba a ɓangaren.

Ya ƙara da cewa, kwamitin ya aika da saƙo ga masu-ruwa-da-tsaki kan cewa su bayar da takardu masu muhimmanci game da batun kafin ranar da za’a tattauna shi a majalisa wanda aka tsara za a yi a majalisar daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Satumba, 2024.

By Babaji