Zanga-zanga: Lauyoyin Obi sun buƙaci Onanuga ya janye kalamansa ko ya fiskanci shari’a 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi ya bai wa Mista Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, sa’o’i 72 da ya biya Naira biliyan 5 a matsayin diyya da kuma neman afuwarsa a cikin manyan jaridun ƙasa guda huɗu saboda ɓata suna da cin mutuncin Obi da suka ce ya yi,ko kuma ya fuskanci shari’a

Obi ya buƙaci Mista Onanuga, ya janye zargin da ya yi masa na ƙage, tare da alaƙanta shi da zanga-zangar da aka shirya yi a watan Agusta.

Ku tuna cewa a ranar 20 ga Yuli, 2024, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya yi ikirari a shafinsa @aonanuga1956 cewa, “Magoya bayan Peter Obi su ne mutanen da ke kitsa tashin hankali a Nijeriya kuma ya kamata Obi ya ɗauki alhakin tashe-tashen hankula.”

Obi da ya ke rubutawa ta bakin lauyansa, Cif Aleɗ Ejesieme, SAN na ƙungiyar MADIBA Chambers, ya ce zargin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da na yau da kullum da jama’a da dama a ciki da wajen ƙasar nan ke karantawa, ya ɓata sunan sa da ya yi ta fama da shi a matsayin mutumin da ke tada zaune tsaye lokacin da duk magabatansa suka bayyana cewa yana ƙyamatar tashin hankali ko da a cikin tsananin tsokana.

Lauyan ya rubuta, “Tabbacin abokin aikinmu ne cewa littafin wani shiri ne da aka ƙididdige shi don wulaƙanta shi, izgili, wulaƙanta shi da kuma kunyata shi ta hanyar kimanta kowane memba na jama’a.”

By ukarofi