Ruftawar gini ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku a Jigawa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Akalla mutane uku ne su ka mutu sakamakon ruftawar wani gini a Jihar Jigawa.

Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar Ƴan sandan Jihar, Lawan Salisu Adam ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya na mai cewa wasu huɗu sun samu raunuka.

A wani jawabin, kiwon dabbobi ya haifar da rikici a ƙauyukan Maikambu da Balalashe na Ƙaramar Hukumar Garki inda aka ƙona gidaje biyar tare da raunata mutum shida.

Rundunar ‘Yan sandan ta ce ta kama mutum biyu da hannu a cikin aukuwar rikicin tare da ƙoƙarin kwantar da al’amarin a yankunan da abin ya shafa.

Aukuwar lamuran sun haifar da ɗar-ɗar a tsakanin al’umma inda ake ganin hakan a matsayin barazana ga al’ummar jihar yayin da su ka yi kira da a tsaurara matakan kariya domin kiyaye aukuwar irin haka nan gaba.

By Babaji