Ina ma Tinubu zai yi koyi da Shugaba Biden

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ

Katsam sai ga labarin cewa, Shugaban Amurka, Joe Biden, ya yi wata sanarwa ta bazata, inda ya amsa kiraye-kirayen ’yan jam’iyyarsa na Democrat, har da tsohon mai gidansa, Barack Obama, cewa ya janye da ga neman tazarce.

Wannan ba ƙaramin dattako ba ne da hangen nesa, kuma abinda ya saka shi tarihi a matsayin Shugaban Amurka na biyu tun 1968 da ya janye daga takara.

Wato da Shugaba Tinubu na Nijeriya zai yi irin wannan hangen nesa, ya bi shawarata, wataƙila da ya ceto ƙasar nan daga halin da ta ke ciki kuma har ma ya iya samun damar tazarce, saɓanin Biden.

Idan a cikin ’yan kwanankin nan kafin zuwan ranar 1 ga Agusta, 2024, ranar da matasan Najeriya ke lasar takobi sai sun fito zanga-zanga, Tinubu ya sanar da dawo da tallafin man fetur kuma fetur ɗin ya koma Naira 300, wallahi ’yan Nijeriya za su iya janye wannan zanga-zanga, saboda hakan zai tsayar da hauhawar farashi nan take, sufuri zai yi sauƙi, sannan tattalin arziki da ya tsaya cak zai fara motsawa, talakawa su sami sa’ida.

A wannan shekara an yi kasafin kuɗi na Naira Tiriliyan 28 kuma a makon da ya gabata Shugaba Tinubu ya nemi sahalewar majalisar dokoki, domin ƙarin kasafin kuɗi na wata Naira Tiriliyan 6.2, domin ayyukan raya ƙasa da kuma na yau da kullum da ƙarin albashi. Maimakon haka, wannan Tiriliyan 6.2 a saka ta a tallafin mai domin a sami sauƙin rayuwa, hankula su kwanta sannan shi kuma Shugaban Ƙasa ya zauna da masana tattalin arziki su fito da sabuwar taswira nan da wata shida, wadda za ta nemo wa ƙasar mafita cikin gaggawa.

Amma yanzu yadda al’umma ta fusata a ko’ina, lokaci ne na shugabanni su fahimci raɗaɗinsu maimakon riƙa kauce wa matsala tare da yin kwaskwarima ta hanyar farfaganda ko kama matasa a na kulle su.

Wallahi hakan babu abinda zai yi banda daɗa fusata mutane. Idan mutane su ka fito a fusace kuma to, zanga-zangar na iya ɗaukar salo maras kyau, wanda zai jefa ƙasar cikin mummunan hali.

Yakamata Shugaba Tinubu ya gane cewa, an kai mutane bango na ƙunci, kuma abinda zai kwantar musu da hankali shine rage raɗaɗin da su ke ji. Raba shinkafa babu abinda zai sassauta na halin da ake ciki, saboda ba za a iya bai wa kowane mabuƙaci ba.

Amma dawo da tallafin mai nan take kaɗai zai iya kawo wa talaka sauƙi, kuma babu dalilin da idan a ka gwada abu ba a sami yadda a ke so ba a ce ba za a iya canzawa ba. Sannan mafi mahimmanci shine ita ce kaɗai hanyar da nan take za ta sa talakawa su janye shirinsu na yin zanga-zanga.

Don Allah Baba Tinubu ka ceci talakawanka yadda za ka iya samun damar tazarce a 2027.

By ukarofi