Makarantar firamare ta kimiyya ta Kurmawa ta yi bikin bada kyautuka

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Makarantar firamare ta kimiyya ta musamman ta Kurmawa ta gudanar da taron yaye ɗalibai da raba kyautuka ga haziƙan ɗalibanta karo na biyar.

Da take jawabi a taron wacce ta wakilci shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, Kansilar kula da cigaban al’umma, Hajiya Hadiza Haruna ta yaba wa ƙoƙarin shugabar makarantar Hajiya Umma Dauda Raula bisa jajircewarta wajen inganta koyarwa da tsaftar makarantar, ɗalibai sun nuna suna fahimtar abinda ake koya musu.

Ta ce Ƙaramar Hukumar Birni da Jihar Kano ƙarƙashin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf suna duk abinda ya kamata wajen yi wa ilimi kyakkyawan tanadi yanzu Ilimi ya soma karsashi saboda kulawa da gwamnati take tare da yaba wa gudummuwar da tsofaffin ɗalibai da masu hali ke bai wa makarantar.

Hajiya Hadiza Haruna ta ja hankalin malamai su kula da tarbiyyar yara da suke a matsayin amana a wajen su, su kuma iyaye su riƙa kula da ‘ya’yansu ta zuwa ziyara makaranta don sanin halin da ilimin ‘ya’yansu ke ciki.

Shi ma sakataren ilimi na ƙaramar hukumar Birnin Kano, Kwamared Nura Sulaiman ya bayyana  cewa shi aka yi wa wannan taro domin shine karon farko na taron ɗalibai da ya soma zuwa taro tun daga naɗa shi akan muƙamin

Ya ce abin da ya gani shugabar makarantar ta yi ƙoƙari kuma makarantar na daga wacce suke alfahari da ita a ƙaramar hukumar Birni nan gaba ma, za a ga abubuwa da dama na inganta Ilimi domin zuwansa sun samar da kayan aiki ga makarantu.

Ya yi kira ga iyaye su ƙarfafa ‘ya’yansu akan zuwa makaranta domin karatu a Kano yanzu kyauta ne ba kuɗi ake biya ba, idan kuma akayi kwatanci da abubuwa da ake a makarantun gwamnati ana masu zaman kansu ma ba a yi domin gwamnati ta samar da malamai ingantattu akwai  yalwataccen filin makaranta da ajujuwa. Su kuma yara ya ce su maida hankali akan karatu gwamnati ta bayar da littatafai da kayan makaranta da abinci da duk abinda ake buƙata na koyo da koyarwa.

Kwamared Nura Sulaiman sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Birni ya yaba da irin gudunmawa da Gwamnatin Jihar Kano da shugaban ƙaramar hukumar Birnin Hon. Sani Chilla da shugaban hukumar SUBEB suke bayarwa na kulawa da cigaban ilimi.

Ita ma shugabar makarantar firamare ta kimiyya ta musamman ta Kurmawa, Hajiya Umma Dauda Raula ta gode wa Gwamnatin Kano bisa ƙoƙarinta na ɗabbaƙa ilimi da farfaɗo da shi ta  kuma yaba da gudummuwar iyayen yara wajenbata goyon baya wajen shirya yin taron duk shekara wannan karo shine na biyar da suke taron bada kyautuka da karrama mutane da suke taimakawa makarantar.

Ta ce  sun karrama shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano da sakataren Ilimi akan ƙoƙarinsu na bibiyar yanda suke gudanar da ayyuka sun kuma karrama tsoffin ɗalibai bisa gudummuwa da suke basu.

Hajiya Umma Dauda Raula ta yi kira ga shugaban ƙaramar hukumar Birni da  Gwamnatin Jihar Kano su kawo musu ɗauki domin maganta matsalar ruwa da suke fama da shi a makarantar  sannan a raƙa bada horo na sanin makomar aiki ga sabbin malamai da aka ɗauka.

Hajiya Umma Dauda Raula ya ce ɗalibai  da aka baiwa kyautuka sun haɗa da ‘yan ajin ƙananan yara da ‘yan aji shida kowane aji an ɗauki masu kwazo daga na ɗaya zuwa na huɗu. Ta kuma  godewa Allah  bisa kwazon ɗalibansu suna kuma irin samun goyon baya da suke daga iyayensu da malamai da ke aiki tuƙuru wajen taya ta cimma burin nasara  da take samu.

Shi ma Alhaji Aminu Bala Usman  shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na makarantar Kurmawa ta ƙasa ya ce  sun gode Allah bisa irin nasarori na cigaba da makarantar ke samu c sun sami Ilimi da tarbiyya a lokacinsu shi yasa basa mantawa da makarantar yanzu Kuma muhallin makarantar ya yi kyau an mayar da ita ta kimiyya ana inganta karatu.

Ya ce duk wani abu da ake gani  ya haskaka makarantar yanzu  akwai gudummuwar ƙungiyar tsofaffin ɗalibai wajen tallafawa cigabanta a fannoni daban-daban sun gina rukunin banɗakuna da sanya intalok da samar da kwamfutoci da wajen koyon sana’o’i da abubuwa da dama.

Alhaji Aminu Bala ya ce tsofaffin ɗalibai na Kurmawa idan za su ɗauki nauyin rushe makarantar a sake ginawa za su iya  amma abinda suke buƙata shine azo a riƙa taimaka mata a ƙara ruɓanyawa akan abinda ake.

Shi ma Alhaji Kabiru Lawan shugaban al’umma gatan makaranta na furamaren kimiyya na kurmawa ya yaba da gudummuwar da al’umma ke bayarwa wajen taimakawa makarantar wajen samun ingantaccen Ilimi kuma shugabar makarantar na aiki tuƙuru.

Ita ma mataimakiyar shugabar iyaye da malamai ta makarantar Aisha Adam ta ce shugabar makarantar Hajiya Umma Dauda Raula tana ƙoƙarin wajen kyautata Ilimi da tarbiyya a makarantar haka suma ƙungiyar iyaye da na tsoffin ɗalibai suna bada gudunmawa. Sai dai suna kira ga Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kawo mu su ƙarin malamai da masu gadi da gyara makarantar da sama musu ruwa domin  da kuɗin aljihunta shugabar makarantar ke sayan ruwa da ɗalibai ke amfani da shi a makarantar don haka a taimaka a kawo mata ɗauki don magance matsalar.

By ukarofi