Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin titin Magami-Ɗansadau

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya hannu kan fara aikin hanyar Magami zuwa Ɗansadau wacce za ta kai tsawon kilo mita 108.

Gwamnan ya gabatar da hakan ne a yayin zama da Majalisar Zartarwar Jihar a Fadar gwamnatin Zamfara a ranar Litinin.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, hakan na zuwa ne la’akari da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar ke yi kan matsalolin tsaro da ya addabi mutanen yankin.

Dauda Lawal, “ya ƙaddamar da ƙwantiragin aikin ga kamfanin Gini na Ɗantata da Sawoe kasancewar sa wanda ya caji kuɗi mafi ƙaranci kuma da zai yi aikin cikin mafi ƙarancin lokaci – watanni 18 akan N81,189,223,505.73” inji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ƙunshi batun kasafi, wanda ya na ɗaya daga cikin abubuwan da aka tattauna a zaman.

Bugu da ƙari, tsarin aikin ya ƙunshi kankare tsawon hanyar, cire duk wani abu mara nagarta tare da maye gurbinsa da mai nagarta, samar na’urar tace wuraren da za a shimfiɗa titin da sauran abubuwan za su taimaka wajen samun aiki mai inganci da nagarta.

By Babaji