
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da ake shirin fara zanga-zangar tsadar rayuwa a gobe Alhamis, babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta taƙaice wa ƴan zanga-zanga yin gangaminsu a filin wasa na MKO Abiola a cikin birnin.
Mai Shari’a Sylvanus Oriji ya bayar da umarnin hakan a lokacin da ya ke yin hukunci kan wani saƙon neman maslaha da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shigar.
A cikin takardar, Wike ya buƙaci kotun ta dakatar da shugabannin zanga-zangar biyar daga yin zagaye a kan titina, unguwanni, ofisoshi da wasu wuraren da al’umma ke wasu harkoki a Abuja. Daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ko ma har a gaba , la’akari da yadda kotun ta amince.
Wike ya ƙara da neman kotun ta wajabtawa hukumomin tsaro su tabbatar da cewa shugabannin zanga-zangar sun kiyaye hakan.
Ya ce, la’akari da bayanan sirri da rahotannin ƴan sanda da suka nuna cewa wasu daga cikin jagororin zanga-zangar sun shirya tayar da rikici da lalata kadarorin al’umma gami da tare hanyoyin da za su hana zirga-zirgar mutane da ababan hawa, hakan kan iya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Kazalika, kotun ta umarci masu-ruwa-da-tsaki a cikin batun da su sanar da matsayarsu game da hukuncin a gidajen jarida domin sanin ina aka dosa.
