Wasu dattawan Arewa da masu ruwa da tsaki, sun goyi bayan matasa a kan shirin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da za a gudanar.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Yusuf Usman, Naja’atu Muhammad, Umar Ardo da Salihu Usman a ranar Laraba, inda su ka ce hujjar yin zanga-zangar gaskiya ne.
Sun ƙara da cewa, shugabanni da dama a ƙasar sun kasa magance matsalolin da ke addabar ‘yan ƙasar da dama. Don haka ya zama wajibi a ƙyale mutane su nuna rashin jin daɗinsu a kan yadda a ke tafiyar da al’amuransu.
Sun yi kira da a guji amfani da jami’an tsaro domin cin zarafin waɗanda za suyi zanga-zangar. Domin doka ta bada damar yin haka.
Sannan sun yi kira da matasa da su guji tashin hankali da zai jawo asarar rayuka da dukiyoyi a yayin da suke gudanar da zanga-zangar.
