Ofishin Jakadancin Amurka, ya umarci ma’aikatansa da su zauna a gida tsawon kwana biyu saboda zanga-zangar matsi na rayuwa da za a gudanar a Nijeriya.
A wani saƙo da ofishin ya aika wa ma’aikatan na sa, ya umarci ma’aikatan su zauna a gida har sai an ce su dawo. Yayin da wanda ayyukansu ba sa yankewa, a ka buƙaci su yi aiki yau Alhamis da Juma’a.
Jami’an tsaro a ƙasar sun nuna damuwa sosai matuƙa, domin ba su son irin abinda ke faruwa a Kenya, ya maimaita kansa a ƙasar.
