Gwamnatin Jihar Borno ta sanya dokar hana zirga-zirga

Spread the love

Gwamnatin Jihar Borno ta sanya dokar hana zirga-zirga a faɗin Jihar.

Wannan ya biyon tashin wani bom a ranar Laraba a kasuwar Kawori, wanda ake zargin ƴan ƙungiyar boko haram ne suka saka.

Bom ɗin yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkata wasu su ma.

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Borno, Nahum Kenneth Daso, shi ya sanar da sanya wannan dokar, inda yace gwamnan Jihar Babagaba Zulum bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki ya ga ya dace a sanya wannan dokar domin dawo da zaman lafiya da lumana a jihar.

Ya na mai roƙon mutanen jihar za su bada haɗin kai domin ganin an samu zaman lafiya a faɗin jihar.

By ukarofi