
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A cigaba da gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, aƙalla manyan motoci ƙirar ‘Bus’ guda bakwai ne aka ƙona a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke jihar Yobe.
An ƙona motocin ne a sakatariyar Ƙaramar Hukumar a ranar Alhamis.
Wani shaida ya ce wasu mutane da su ka yi dandazo sun yi ƙoƙarin haddasa rikici a wajen yayin da jami’an tsaro su ka gaggauta dakatar da su.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘Yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya na mai cewa za a hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.
Kasancewar haka, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita na tsawon kwana ɗaya a ƙananan hukumomin Potiskum, Gashua da Nguru inda wasu ɓata-gari ke amfani da damar hakan wajen satar kayan gwamnati da kuma al’umma.
