Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan majalisa 15 a ƙarƙashin ƙungiyar The Economy Rescue Group, sun yi kira shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, da ya yi murabus.
Ƙungiyar ta yi zargin rashin gudanar da ayyukanta a ƙarƙashin jagorancin Kyari a NNPCL ne ya haddasa matsaltsalun da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ciki.
A wata sanarwa da shugaban ta Hon. Esosa Iyawe, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Oredo a majalisar wakilai a Abuja ya sanyawa hannu a Abuja, ‘yan majalisar sun dage cewa a dakatar da Kyari, har sai an samu sakamakon kwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai kan harkokin man fetur na ƙasa dake bincike kan halin da kamfanin mai na ƙasa ke ciki da kuma sassan ƙasa gaba ɗaya.
‘Yan majalisar dai sun zargi shugaban kamfanin na NNPC da sauran ma’aikatan hukumar da yin zagon ƙasa ga Ajandar Tinubu ta hanyar cin hanci da rashawa da rashin iya aiki har sai an kammala binciken da majalisar wakilai ta fara ta hanyar kwamitin haɗin gwiwa.
