Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, wanda shi ne kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ya fito ƙarara ya shaida wa ma’aikatan jihar cewa gwamnatin sa ba za ta iya biyan Naira 70,000 mafi ƙanƙantar albashi ba.
Ya bayyana haka a ranar Talata, lokacin da ya yi taro da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago, ƙungiyoyin ayyukan kare haƙƙi da na ‘yan tireda, a Fadar Gwamnatin Gombe.
Ya gana da su ne inda ya shaida masu gaskiya, kwana biyu kafin zuwan ranar 1 ga Agusta, ranar da matasan Nijeriya suka yanke fitowa zanga-zanga.
Gwamna Yahaya ya ce ɗan kuɗin da jihar ke karɓa duk wata daga hannun Gwamnatin Tarayya ba za su isa a riƙa biyan Naira 70,000 mafi ƙanƙantar albashi ba.
“Ni dai ba zan iya biyan mafi ƙanƙantar albashi ba. Kuma ina zaton wasu jihohi da yawa su ma ba za su iya biya ba. Mu da su duk jirgi ɗaya ya kwaso mu,” haka dai gwamnan ya bayyana.
Daga nan ya riƙa jero irin ƙalubalen ƙarancin kuɗin shiga da jihar Gombe ke fuskanta.
Ya ce hatta waccan Naira 30,000 mafi ƙanƙantar albashi ita ma da kyar da gumin goshi wasu jihohi ke iya biya.
Ya ce to yanzu kuma yadda komai ya yi tsada ya sa ita kan ta Naira 30,000 abu ne mai wahala, ballantana kuma Naira 70,000.
Gwamnan ya ci gaba da cewa har yau Jihar Gombe na zaman jiran isowar tirela 20 na kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta raba wa jihohi na shinkafa, domin a raba wa talakawa.
Ya ce Jihar Gombe ta karɓi Naira biliyan 2 kacal daga gwamnatin tarayya da sunan tallafi, ba Naira biliyan 5 da aka riƙa yayatawa ba.
Daga nan ya ɗora laifin matsalar cire tallafin fetur wadda ita ce ta haddasa wannan raɗaɗin tsadar rayuwa kan gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya assasa ta, kuma ba a saka ta cikin kasafin 2023 da Shugaba Bola Tinubu ya taras ba.
Ya ce Tinubu ya sanar da cire tallafin fetur ne, saboda gwamnatin Buhari ba ta saka tallafin a cikin kasafin 2023 ba.
Ya ce Tinubu ba shi da zaɓi ko wani laifi da ya cire tallafin fetur, saboda babu yadda zai yi a lokacin. Babu tallafin a cikin kasafin 2023 na Buhari na ƙarshe, kuma a lokacin da Tinubu ya hau ba a kafa sabuwar Majalisa ta 2023 zuwa 2027 ba.
