Ribadu ya miƙa mutanen da aka ceto hannun ‘yan bindiga ga iyalansu a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu, ya damƙa mutum biyar da jami’an tsaro suka kuɓutar daga sansanin ‘yan bindiga.

Ofishin Ribadu, (wato ONSA) ne ya tsara yadda aka samu nasarar kuɓutar da mutanen ‘yan gida ɗaya.

Ribadu ya ce an damƙa iyalan Sanda Bitrus, ciki har da matarsa, wani matashi dai an yi garkuwa da su ne a ranar 20 ga Yuli, a ƙauyen Mahuta, cikin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu, a Jihar Kaduna.

Ya ce ofishin sa ne ya tsara yadda aka samu nasarar kuɓutar da su tare da haɗin guiwar sauran ɓangarorin jami’an tsaro, waɗanda suka kuɓutar da mutanen a ranar 28 ga Yuli.

Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta na bakin ƙoƙarin ganin ta samu nasarar magance matsalolin tsaro, kuma ta sha alwashin ceto dukkan mutanen da ke hannun ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran mugaye.

Ya jinjina wa jami’an tsaro kan namijin ƙoƙarin da suke yi domin ganin an daƙile matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.

“Mun yi ƙoƙari sosai, kuma muna ci gaba da ƙoƙari, amma da yake a cikin sirri muke cikin mu.

“Muna godiya kan jajircewar daki ke kuna aiki tuƙuru, domin domin samar da zaman lafiya a ƙasar mu. Allah zai yi maku kyakkyawar sakayya.

“Wannan aiki ne mai wahala, aiki da mutane ba su ma san ana yin sa ba, amma abubuwa da yawa na faruwa.

“Dubban mutane sun sami ceton kuɓutar da su daga hannun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sakamakon wannan aiki da muke yi. Ina godiya sosai ga jami’an tsaro,” inji Ribadu.

By ukarofi