Ina goyon bayan harajin da Tinubu ya saka wa bankuna – Otedola

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Gamayyar Kadarorin Bankin First Bank, Femi Otedola, ya bayyana goyon bayan sa ga gwamnatin Bola Tinubu dangane da sabon harajin da za a ƙaƙaba wa bankuna, wanda za su riƙa biya duk shekarar da banki ya ci ƙazamar riba.

Cikin wata sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES a ranar Laraba, biloniya Otedola ya kuma ragargaji shugabannin bankuna a ƙasar nan masu bushasha da facaka da almubazzaranci da kuɗaɗe, lamarin da ya kai har su na gasar sayen jiragen shiga na su na kan su.

“An wayi gari wasu shugabannin bankuna a ƙasar nan sun fi fifita jin daɗin rayuwar su fiye da kulawa da haƙƙin masu hannayen jari a bankin da kuma kwastomomin su,” inji Otedola.

“Wato ni ina adawa masu almubazzaranci da wadaƙa da dukiya, musamnan masu kamfatar kuɗaɗe su na sayen jiragen sama na hawa don wauta.

“Bankunan Najeriya su na kashe Dala miliyan 50 duk shekara wajen hidimar kula da jiragen su na sama. Kuma bankuna huɗu sun kashe dala miliyan 500 wajen sayen jirage 9.”

Makonni biyu da suka gabata ne Gwamnatin Tinubu ta ce za ta ƙaƙaba wa bankuna Harajin Cin ƙazamar Riba.

Shugaba Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa da ta Tarayya su yi wa Dokar Kuɗaɗe ta 2023 garambawul, ta yadda za a ƙirƙiro Harajin Cin ƙazamar Riba kan bankunan kasuwancin ƙasar nan.

Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aika wa Majalisa a ranar Laraba, wadda a ciki ya nemi amincewar su da ya ƙara lafta Naira tiriliyan 6.2 cikin kasafin 2024.

Gwamnatin Tarayya ta ce ta lura a duk ƙarshen kowace shekara bankuna na cin ƙazamar riba, ‘dalili kenan ma ake ta rige-rige da takarar kafa bankuna barkatai a faɗin ƙasar nan.”

Wannan batun fara karɓar Harajin Cin ƙaramar Riba kan bankunan Najeriya ya zo ne a ranar da Premium ta buga cewa Bankin Zenith ya ce ya na sa ran cin ribar Naira tiriliyan 1 a cikin 2024.

A cikin labarin, wannan jarida ta buga cewa Bankin Zenith ya kama hanyar cin ribar Naira tiriliyan 1 cikin 2024, yayin da Bankin Jaiz ke gaganiyar haɗa jarin Naira biliyan 20.

Zenith Bank ya ƙudiri aniyar cin zunzurutun riba ta Naira tiriliyan 1 a cikin 2024.

Babbar Jami’ar Zenith Bank, Adaora Umeoji ce ta bayyana haka a wani taron masu hannayen jari da manyan kwastomomin bankin da aka yi a Legas, cikin makon da ya gabata.

Ta ce a yanzu haka bankin na da zunzurutun madarar kuɗi har Naira tiriliyan 1.8, yayin da kuɗaɗen masu hannayen jari a bankin ya kai Naira tiriliyan 2.3, sai kuma ƙarfin kuɗaɗen hada-hadar kasuwanci har Naira tiriliyan 1.3.

Ta ce a cikin 2023 Zenith Bank ya ci ribar Naira biliyan 796 kafin a cire kuɗaɗen haraji a cikin adadin ribar.

Ta ce idan aka yi la’akari da yadda bankin ya ci ribar Naira biliyan 796 a cikin 2023, to su na kyautata zaton a ahekarar 2024 za a sami ribar Naira tiriliyan 1.

Ta ce ya yi wannan kyakkyawan hasashen ne bisa duba da cewa tsakanin watannin Janairu, Fabrairu da Maris na farkon 2024, bankin har ya ci ribar Naira biliyan 320.

Wannan ya na zuwa ne daidai lokacin da Bankin Jaiz ke gaganiyar haɗa ƙarfin jarin kuɗaɗen hada-hada zuwa Naira biliyan 20 kacal.

Manhaja ta ruwaito Bankin Jaiz na cewa, ‘Mu za mu riga kowane banki fara cika ƙa’idar ƙara yawan kuɗaɗen hada-hada’.

Bankin Jaiz ya bayyana cewa saura ƙiris ya rage ya cika umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN) na tabbatar da cewa adadin kuɗaɗen hada-hadar bankin sun kai Naira biliyan 20.

Babban Jami’in Bankin Jaiz, Haruna Musa ne ya bayyana haka a ranar Talata, yayin da yake jawabi a Taron Shekara-shekara na Masu Hannayen Jari, inda ya ce tuni har masu hannayen jari sun zabga Naira biliyan 10.

Musa ya ce Bankin Jaiz ne zama na farko wajen cika sharuɗɗa da ƙa’idojin da CBN ya gindiya.

“Mu ne za mu fara cika sharuɗɗa da ƙa’idojin da CBN ya gindaya kan adadin yawan ƙarfin kuɗaɗen hada-hadar da aka gindiya wa kowane banki.”

A ƙarshen watan Mayu ne dai Premium Times Hausa

CBN ya umarci bankunan kasuwanci su ƙara yawan kuɗaɗen hada-hadar su.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan Najeriya cewa kowane ya ƙara yawan jarin kuɗaɗen hada-hadar sa.

An buƙaci bankunan cewa kowane ya tabbatar da ya ƙara aƙalla adadin da aka umarce shi ya ƙara, nan zuwa watanni 24 masu zuwa.

Cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta Riƙo ta CBN, Hakama Ali ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ana buƙatar ƙarfin jarin duk wani banki mai rassan hada-hada a ƙasashen waje ya kasance Naira biliyan 500, yayin da bankunan cikin ƙasa kawai ya kasance ƙarfin na da ƙarfin ƙarin Naira biliyan 200.

CBN ya ce ƙananan bankuna da ke yankunan ƙasar nan daban-daban kuma, na su ƙarfin jarin kada ya gaza Naira biliyan 50.

CBN ya ce an umarci kowane banki ya cika waɗannan sharuɗɗa nan da tsawon watanni 24 daga ranar 1 ga Afrilu. Wato kada wani banki ya wuce ranar 31 Ga Maris, 2026 bai cika sharuɗɗan ba.

By ukarofi