Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan sanda sun yi harbe-harbe bayan matasa sun yi fito-na-fito da su a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a safiyar Alhamis a Jihar Neja.
Jami’an tsaro sun ɗauki matakin ne bayan matasan sun yi yunƙurin toshe hanya a yankin Tunga da ke garin Minna.
Bayan ’yan sanda sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa su, daga bisani matasan sun sake taruwa suna neman sake rufe hanyar.
A lokacin da wakinmu ya isa wurin da misalin ƙarfe 9 na safe, ya iske ’yan sanda da ’yan banga suna ƙoƙarin janye duwatsun da matasan suka tare hanya.
A lokacin kuma masu zanga-zangar da ’yan kallo suna guje-guje bayan iska ta turnuƙe da hayakƙin da jami’an tsaron suka harba.
An kuma girke jami’an tsaro iri-iri a wurare daban-daban da ake zargin yiwuwar samun barazanar tsaro.
Daga cikin wuraren har da shataletalen Kpakungu da ke kan hanyar Minna-Bida, ind a baya aka yi irin wannan zanga-zanga.
Masu shaguna da kasuwanni sun kasance a rufe domin guje wa harin ɓata-gari.
