Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani matashi ɗan shekara 29, Mizanmil Abubakar, ya kashe mahaifinsa, Abubakar Adawa, mai shekaru 65, bisa zargin masu kawo masa matsala a harkokinsa a unguwar Kpakungu da ke Minna, Jihar Neja.
Wanda ake zargin, kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya kuma daddatsa gawar mahaifin nasa gunduwa-gunduwa, ya tattara su a cikin buhun siminti sannan ya binne shi a wani rami mara zurfi a cikin gidan su.
An gano cewa Abubakar Adawa mai shekaru 65 ‘yan uwansa ne suka kai rahoton ɓacewarsa a ofishin ‘yan sanda na Kpakungu a ranar 30 ga Yuli, 2024.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a Minna Laraba.
Ya ce: “A ranar 30/7/2024 da misalin aarfe 10 na safe, an samu labari a Kpakungu Diɓ cewa a ranar 29/7/2024, wani Abubakar Adawa mai shekara 65 ya ɓace a gidansa da ke unguwar Barkin-sale a Minna.”
Ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda da ke aiki a Diɓ ƙarƙashin jagorancin DPO sun ziyarci gidan, yayin da aka gayyaci ‘ya’yansa Mizanmil Abubakar da Aisha Abubakar, da mahaifiyarsu domin yi musu tambayoyi.
“Duk da haka, an yi bincike sosai a gidan, kuma abin mamaki, an gano gawar wanda ya ɓace an binne shi a wani kabari mara zurfi a cikin gidan,” inji shi.
Ya ce, ɗan ya bayyana cewa shi ne ya aikata wannan ɗanyen aikin kuma marigayi mahaifins yana tsananin nuna masa aiyayya, don haka ya yi amfani da fartanya ya kashe shi ya yanka shi sassa kafin ya binne shi a wani kabari mara zurfi a gidan
