Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya bayyana cewa babu wani laifi ko haƙ ƙ i da ke kan wuyan Shugaban ƙasa Bola Tinubu, saboda ya cire tallafin fetur.
Da yake wa shugabannin ƙ ungiyoyin Jihar Gombe jawabi a ranar Talata a Gidan Gwamnati, Yahaya ya ce tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya cire tallafin fetur, saboda babu kuɗin tallafin fetur a cikin kasafin Buhari na ƙarshe na 2023, wanda Tinubu ya taras a ranar 29 ga Mayu.
Ya ce Tinubu ba shi da yadda zai yi sai dai ya cire tallafin kawai, domin babu kuɗin a cikin kasafin 2023 wanda Buhari ya sa wa hannu kafin ya kammala wa’adin mulkinsa.
Gwamna Yahaya ya ce lokacin da Tinubu ya hau mulki ba a kafa majalisa ba, ballantana ya hanzarta kai mata ƙudirin amincewa da ƙ arin kasafi.
Ya ce wannan cire tallafin ne ya janyo matsananciyar tsadar rayuwa da ake fuskanta a yanzu, wadda wasu da dama ke ganin cewa laifin Tinubu ne, amma a gaskiya ba laifinsa ba ne.
Da ya koma kan batun ƙarin kuwa, Gwamna Yahaya ya ce ba zai iya biyan N70,000 mafi ƙanƙantar albashi ba.
Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, wanda shi ne kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ya fito ƙ arara ya shaida wa ma’aikatan jihar cewa gwamnatinsa ba za ta iya biyan Naira 70,000 mafi ƙ anƙ antar albashi ba.
Ya bayyana haka a ranar Talata, lokacin da ya yi taro da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago, ƙungiyoyin ayyukan kare haƙƙi da na ‘yan tireda, a Fadar Gwamnatin Gombe.
Ya gana da su ne inda ya shaida masu gaskiya, kwana biyu kafin zuwan ranar 1 ga Agusta, ranar da matasan Nijeriya suka yanke fitowa zanga-zanga.
Gwamna Yahaya ya ce ɗan kuɗin da jihar ke karɓa duk wata daga hannun Gwamnatin Tarayya ba za su isa a riƙa biyan Naira 70,000 mafi kanƙantar albashi ba.
“Ni dai ba zan iya biyan mafi ƙ anƙ antar albashi ba. Kuma ina zaton wasu jihohi da yawa su ma ba za su iya biya ba. Mu da su duk jirgi ɗaya ya kwaso mu,” haka dai gwamnan ya bayyana.
