Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Alhaji Ismail Sa’adu Usman, Dagacin unguwar Ja’en da ke ƙ aramar hukumar Gwalle Jihar Kano ya yaba wa makarantar Islamiyya ta Al-ansar Islamiyya wacce ke ƙarƙashin shugabancin Malam Bashir Abdullahi Ja’en wacce ta yi walimar ɗalibai 168 wanda suka sauke Alƙ ur’ani mai girma a wannan lokaci ya kuma ce akwai buƙ atar iyayen yara da sauran mawadata su riƙ a taimakawa irin waɗanan makarantu na addini dama sauran makarantu masu koyar da sana’o’i da ilimin zamani a cewar dagacin Ja’en Alhaji Ismaila Sa’adu Usman, kamar dai yadda ya bayana a ranar Lahadi da aka gabatar da saukar a masallacin Ado Bayero da ke unguwar Ja’en ƙaramar hukumar Gwalle Kano.
Haka kuma ya ce Unguwar Ja’en tana da unguwanni sama da goma kuma yanzu ana zaune lafiya duk da yawan ƙabilu daban-daban da ta ke da shi ko matsalar kwanaki da akai ta yayatawa matsalar kafofin sadarwa na zamani ne da sauransu unguwa ɗaya ce matsalar ta afku, cikin unguwani sama da 12 amma yanzu komai yawa wucce da taimakon Allah da gudumawar shugabani da hukumomin tsaro.
Shi ma a jawabinsa shugaban makarantar Al-ansar ya ce wannan rana ranar farin ciki ne da aka yaye ɗalibai a wannan karo wanda ba shi ne na farko ba kuma suna farin ciki da jin daɗi yadda al’ummar wannan yanki bisa jagorancin Dagacin Ja’en da sauran shugabanin al’umma, ke ba su haɗin kai na zaman lafiya da gudanar da wannan karatu cikin kwanciyar hankali da haɗin kai.
Shi ma Malam Adamu Abubakar Adamu Ajingi Hisba, ya bayyana jin daɗinsa da wannan walima ta ɗaliban makarantar, inda kuma ya bayana Dagacin Ja’en a matsayin shugaba mai dattaku da kyakkyawar mu’amala a wannan yanki.
Shi ma Alhaji Kabiru Salisu Hamdala Bired, ya ce kano cibiyar addini ce kuma cibiyar kasuwanci da sarauta da noma ne su ne tushen ɗaukakar Kano kiransu da gwamnan Kano da Bola Tinubu, da sauran masu ruwa tsaki shi ne a sassauto da farashin kayan abinci musamman shinkafa masara fulawa da sauransu domin tsaka ta sa an rufe ƙananan masana’antu a Kano da ƙasa baki ɗaya.
