An sassauta dokar fita a Kano da Yobe

Spread the love

Gwamnatocin jihohin Yobe da Kano sun sassauta dokar hana fita ta sa’o’i ashirin da huɗu da suka kafa a wasu garuruwa.

In bamu mance ba, gwamnatocin sun sanya dokar hana fita bayan zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki da ta rikiɗe ta koma tashin hankali

A wani jawabi da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Baba Ɗantiye ya sanar a ranar Lahadi, ya ce dokar hana fita a jihar yanzu ta fara daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 2 na rana.

Ya ce an gyara dokar hana fita ne domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Dantiye ya ce Gwamna Abba Yusuf na jihar ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwa da dukiyoyi a zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa tashin hankali.

Ya kuma ce gwamnan ya buƙaci mazauna jihar da su koma gidajensu da misalin karfe 2 na rana, yana mai ba su tabbacin cewa za a sake duba dokar hana fita “saboda yanayin tsaro ya inganta”.

Ya ce gwamnan ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da yi wa jihar da ƙasa addu’ar zaman lafiya, ci gaba da samun kwanciyar hankali a siyasance.

Hakazalika, bayan wani gagarumin ci gaba a harkokin tsaro a Potiskum, Gashua, da Nguru, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da sake duba dokar hana fita da aka kafa a garuruwan uku na tsawon sa’o’i biyar.

Birgediya Janar mai ritaya. Ɗahiru Abdulsalam, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.

Yanzu haka an sassauta dokar hana fita daga rana zuwa karfe 5 na yamma domin baiwa mutane damar gudanar da ayyukan su daga ranar Lahadi.

Yayin da yake yabawa jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi na maido da zaman lafiya a yankin, gwamnan ya buƙaci da su ci gaba da taka tsan-tsan tare da daƙile duk wani abu da ya shafi doka da oda a lokacin da aka sassauta dokar hana fita.

Ya kuma umarci mazauna garin da su ba jami’an tsaro haɗin kai tare da kai rahoton duk wani abu da suka saɓa da shi.

Ya kuma bai wa al’umma tabbacin ci gaba da jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaro da jin daɗin ‘yan ƙasa baki ɗaya.

An fara zanga-zangar cikin lumana amma ta rikiɗe zuwa tashe tashen hankula a jihohi da dama da suka haddasa asarar rayuka da ɓarnata dukiya.

By ukarofi