Harbin masu zanga-zanga: Atiku ya kai Tinubu gaban Majalisar Ɗinkin Duniya da Kotun Duniya

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya kuma jagoran jami’iyyar adawa ta PDP yayi Allah wadai da buɗe ma masu zanga-zangar lumana da jami’an tsaro su ka yi a garuruwan Abuja da kano.

Atikun yace, dole jami’an tsaro su ba ƴan ƙasa kariya a lokacin da suke gudanar da zanga-zanga domin tsarin doka ya basu dama.

Amma abin kunya ne yadda waɗanda ya kamata su ba da tsaro, sune suke buɗe ma mutane wuta yayin da suke aiwatar da abin da doka ta basu dama.

Atikun yayi kira da Majalisar Ɗinkin Duniya da kotun manyan laifuka na duniya ta sanya idanu a Nijeriya domin ganin an gurfanar da waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin.

Yace dole shugaba Tinubu ya fito ya nuna shi jagora ne domin fito da Nijeriya cikin wannan halin kunci da matsi da ake fama dashi.

By ukarofi