Muhimman batutuwan tattalin arziki da jawabin Shugaba Tinubu ya ƙunsa

Spread the love

Muhimman batutuwan tattalin arziki da jawabin Shugaba Tinubu ya ƙunsa

Jawabin Shugaban Ƙasa Tinubu ya ƙunshi wasu muhimman batutuwa a kan tattalin arziki Nijeriya. Waɗannan batutuwa su ne:

  1. Cire tallafin man fetur da dala domin liƙe hanyoyin fitar kuɗi.
  2. Samun ƙari a kan harajin da gwamnati ke amsa wanda ya haura tiriliyan 9.1 a watanni ukun farkon 2024
  3. Raguwar biyan bashi da haraji daga kasa 97% zuwa kaso 67 a cikin watanni 13
  4. Biyan bashin dala ga mutane da kamfanoni wanda aƙalla ya kai dala biliyan biyar
  5. Manyan ayyukan gina ƙasa kamar titin Lagos-Calabar da kuma Sokoto- Badagry
  6. Sauyi a harkokin man fetur da ya jawo zuba hannun jari na aƙalla dala miliyan 500.
  7. Ƙaddamar da motocin da suke amfani da iskar gas CNG domin rage raɗaɗin cire tallafi
  8. Fito da tsarin bada lamuni ga ɗalibai da ke manyan makarantu
  9. Samar da aƙalla dala 620 domin ga harkokin yanar gizo da kwamfuta domin samar ma matasa ayyukan yi
  10. Ƙirkirar Cibiyoyin koyar da sana’o’i daban daban a faɗin ƙasar nan.
  11. Bayar da dala 500 ga jihohi domij rage raɗaɗin matsin rayuwa da ake fuskanta da kuma bayar da bashin Naira miliyan ɗaya ga ƙananan sana’o’i guda 75,000
  12. Ƙaddamar da tsarin ginin rukunin gidaje 100,000 domin samar da ayyukan yi
By ukarofi