Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya yi magana kan cire tallafin man fetur

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur da rushe tsarin cinikayyar ƙasashen waje ne sakamakon koma baya da hakan ke haifar wa cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.

Tinubu ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabin kai-tsaye game da zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya, ya na mai cewa tattalin arziƙin ƙasa na fuskantar matsalolin durƙushewa tsawon shekaru saboda rashin tsare-tsare da ɓangaren ya fuskanta.

Tinubu ya ce, “sama da shekara ɗaya, Nijeriya ta kai wani mataki da ba za ta iya amfani da tsare-tsare na wucin-gadi wajen magance matsaloli masu dogon zango ba da za su amfani al’umma a yanzu da ma nan gaba.”

Saboda haka, ya ce “matakan sun taimaka wajen dakatar da son kai da riba da ƴan jari-hujja su ke samu. Sun kuma toshe ƙofofin bayar da tallafin da ba bisa tsari ba ga ƙasashen maƙofta waɗanda hakan ma sun taimaka wajen durƙushewar tattalin arziƙin Nijeriya.”

Kazalika, ya ce matakan da ya ɗauka su na da muhimmanci wajen daidaita taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasa, don haka ya na tabbatar wa al’umma cewa ya mayar da hankali wajen ganin an samu kyakkyawar gwamnati ga al’ummar Nijeriya.

By Babaji