Daga JAMIL GULMA, a Birnin Kebbi
Wani ruwan sama da aka yi kama da bakin ƙwarya a waɗansu sassan Jihar Kebbi da aka soma tun ranar Juma’ar da ta gabata zuwa ranar Lahadi ya yi sanadiyyar rushewar gidaje sama da ɗari200, inda kimanin sama da mutane 700 suka rasa matsuguni, musamman a ƙananan hukumomin Argungu da Augie.
Ruwan saman ya yi ƙamari a daren Lahadi, wanda ya sanya dole magidanta a ƙauyen Kamfani mai kimanin kilomita 10 daga Argungu kan hanyar Sakkwato kwasar kayansu zuwa filin Polo da ke kusa da ƙauyen.
Malam Umar Muhammed Kamfani, wani magidanci, ya bayyana cewa tun cikin daren Lahadi ba wanda ya yi bacci, saboda tashin hankalin da suka gani na ruwa da kuma yadda gine-gine ke ta riftawa ba ƙaƙƙaftawa.
Haka dai suka kwana a cikin tashin hankali yayinda tun cikin dare dai waɗansu suka soma kwasar kayansu zuwa filin na Polo musamman masu ginin ƙasa.
Ya bayyana cewa duka da ya ke dai ba a sami hasarar rayuwa a ƙauyen na Kamfani ba amma dai an yi hasarar dukiyoyi na milliyoyi.
Ya nemi gwamnati da ta kawo musu agaji musamman na yatan abinci da magunguna kuma idan zai yiwu a nema musu wani matsuguni da za su koma tare da iyalansu da ya ke ana cikin yanayin damina.
Haka-zalika a ƙaramar Hukumar Mulki ta Augie an sami ambaliyar ruwan sama a garuruwanTiggi cibiyar gundumar ƙasarTiggi da waɗansu sassan gundumar.
Wani magidanci da abin ya shafa daga garin Tiggi ya bayyanawa jaridar Blueprint Manhaja cewa, sun rasa gidajensu da dukiyoyi masu yawan gaske sanadiyyar wannan ruwan, saboda haka suna neman agajin gaggawa daga ‘yan siyasa da hukumomi musamman gwamnatin Jihar Kebbi saboda yanzu haka ba su san inda za su koma da iyalansu ba don asibiti da makaranta da aka ba su ba zai iya ɗauke su ba.
Uban ƙasar Bayawa Alhaji Murtala Muhammad Kaka, ya bayyanawa wakilinmu cewa, a a garin Birnin Tudu gini ya riftawa wata budurwa, sai kuma ƙauyen Jabaka a can ma ginin ne ya riftawa waɗansu ‘yammata biyu ‘yan kimanin shekaru uk zuwa huɗu.
Ya ƙara da cewa, tuni waɗanda abin ya shafa sun koma makarantun firamare da ke garin Bayawa kuma gwamanti da ‘yan siyasa sun kawo agajin kuɗaɗe da kayan abinci da na kwanciya.
Malam Bello Bayawa, ya bayyana cewa, a garin Bayawa da ke ƙaramar Hukumar Mulki ta Augie a can ma an sami iftila’in ambaliyar ruwan inda aƙalla sama da gidaje ɗari da arba’in (140) suka rushe wanda ya yi sanadiyyar rasa matsuguni ga ɗaruruwan mutane. Duk da ya ke dai ba a sami hasarar rayuwa ko ɗaya ba sai dai dabbobi da kuma sauran dukiyoyi.
Ya ce, ‘yan siyasa da hukumar agajin gaggawa ta SEMA sun kawo agajin kuɗaɗe da kayan abinci da kuma na kwanciya.
Mataimakin gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, a madadin maigirma gwamna, ya ziyarci garuruwan da iftila’in ambaliyar ruwan ya shafa, ya jajanta musu tare da bayar da tabbacin gwamnatin Jihar Kebbi za ta ɗauki matakin gaggawa wajen ganin an sama musu matsuguni da kuma abinci.
Ya ƙara da cewa, gwamanti za ta duba yiyuwar sauya wajen zama idan buƙatar haka ta taso.
Jami’in Hulɗa da jama’a na hukumar HYPADEC Malam Nura Tanko Wakili, ya bayyanawa wakilinmu ta wayar tarho cewa, reshen hukumar na Jihar Kebbi bai yi ƙasa a gwiwa ba na zagaya duk garuruwan da iftila’in ambaliyar ruwan sama ya shafa a jihar, kuma sun turo rahoto wanda yanzu haka ana nan ana shirin kai kayan agaji da ake da buƙata na gaggawa kafin a kammala shiri na musamman don bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
Yanzu haka dai ana cigaba da kai kayan tallafi da suka haɗa da kuɗaɗe, da abinci da kayan kwanciya ga sansanonin da abin ya shafa dabam-daban daga gwamnatin Nihar Kebbi da hukumar agajin gaggawa da kuma ‘yansiyasa.
Rahotanni daga waɗansu sassan jihar sun bayyana cewa, ko a kwanakin baya an sami wata ambaliyar mai kama da wannan a ƙananan hukumomin Suru da Bagudo, inda su ma kamar sauran an samu asarar kayan abinci da kuma muhalli.



