Gwamnatin Tinubu ba ta biyan tallafin fetur, inji Ministan Kuɗi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta musanta mayar da tallafin man fetur, inda ta ce babu wani kasafin kuɗin da aka ware mata.

Ministan Kuɗi Wale Edun ya bayyana haka a wata hira da ya yi kwanan baya a gidan talabijin na AIT.

Edun ya ce ba a saka tallafin man fetur a cikin kasafin kuɗin ƙasar na 2024 kuma ya bayyana ci gaban tattalin arziki a matsayin dalilin kiyaye manufofin da ake ciki.

“Babu tallafin mai a kasafin kuɗin. Muna da alamun cewa muna tafiya kan hanyar da ta dace, kuma dole ne mu kiyaye wannan yanayin,” in ji shi.

Shugaba Bola Tinubu a jawabinsa na farko a ranar 29 ga Mayu, 2023, ya bayyana cewa tallafin man fetur ya tafi.

Wannan ci gaban ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin N200 zuwa sama da N600 kowace lita.

A wata hira da jaridar Financial Times, Obasanjo ya caccaki yadda gwamnati ta cire tallafin.

A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta aiwatar da wasu matakai kafin cire tallafin.

Duk da haka, ya bayyana cewa tallafin ya “dawo” saboda yawan hauhawar farashin kayayyaki.

“Akwai ayyuka da yawa da ya kamata a yi. Ba wai kawai ka tashi da safe ka ce ka cire tallafin ba. Saboda hauhawar farashi, tallafin da muka cire bai tafi ba. Ya dawo,” in ji Obasanjo.

Ya kuma bayyana buƙatar amincewar masu zuba jari a Nijeriya, yana mai cewa, “Dole ne ku fita daga tattalin arzikin kasuwanci zuwa tattalin arzikin canji.”

By ukarofi