Gwamnati za ta bada tallafin Naira biliyan 110 ga sana’o’in matasa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta ce ta sauya shirin zuba hannun jari na matasan Nijeriya (NYIF) zuwa ware Naira biliyan 110 da bayar da jari ga masu ƙananan sana’o’i.

Ministar matasa, Dakata Jamila Bio Ibrahim ta faɗi hakan a Akure, babban birnin jihar Ondo a lokacin da ta ke ganawa da matasan Kudu-maso-Yammacin Nijeriya.

Ta ce, an samu sama da matasa 200,000 cikin sati biyu da ke neman amfana da tallafin tun da aka sake kaddamar da shirin NYIF.

Ministar ta kuma ce munafar shirin ita ce samar da sauƙi wajen samun aron kuɗi ga matasan don inganta rayukansu ta fuskar sana’o’i da ma amfanin kai.

“Hakan kuma na nufin ƙara ikon mallakar kuɗi da bayar da gudummawa ga tattalin arziƙin ƙasa, inji ta.”

Haka nan, ta ce za su samar da bankin inganta matasa domin bayar da tallafi ga sana’o’in matasa wanda hakan zai taka rawar gani a gare su da ma tattalin arziƙin ƙasa.

Shugaba Tinubu ya ware kaso 30 na muƙamai a gwamnatinsa ga matasa wanda ya kere matakin tunaninsa ga ƙoƙarin da matasan za su iya.

By Babaji