‘Yan sanda sun zafafa sintiri gabanin zanga-zangar mutum miliya ɗaya a manyan birane

Spread the love

Ɗaruruwan ƴan sanda ne ke sintiri a manyan birane da ke Nijeriya sabida zanga-zangar mutum miliyan ɗaya da ake sa rai za a gudanar a yau Asabar.

Zanga-zangar yunwar da matsin rayuwa a na sa ran za ta ƙare yau.

Masu zanga-zangar na neman gwamnati ta dawo da tallafin mai, ƙara mafi ƙarancin albashi da kuma sauran batutuwa domin kawo sauƙi da ɗan Nijeriya.

Duk da dai zanga-zanga ta rage ƙarfi a jihohi da dama, garuruwa irin su Kano,Kaduna,Ribas da Bauchi har yanzu ana gudanar da ita.

Kodinetan ‘Take It Back Movement ‘ Sanyaolu Juwon ya ce su na nan suna tattara kan ƴan Nijeriya domin yin zanga-zangar mutum miliyan ɗaya a kowanne jihohin tarayyar Nijeriya.

Juwon ya buƙaci a saki masu zanga-zanga da aka kama domin ba su da laifi. Ya bayyana kama masu zanga-zanga da cin zarafin su ba zai sa su daina zanga-zangar ba.

Jihohi irinsu Kano, Abuja, Legas da kuma Ribas an ga ƙarin yawan jami’an tsaro suna sintiri a wurare da dama a sassan jihohin.

By ukarofi