
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙasar Poland da ke Nahiyar Turai ta musanta batun cewa ƴaƴanta da jami’an hukuma suka kama a Kano an same su da laifin ɗaga tutar ƙasar Rasha.
A ranar 6 ga watan Agusta ne aka kama ƴan ƙasar kan zargin ɗaga tutar Rasha a Kano a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da ƴan Nijeriya suka gabatar. Sannan, an kama wasu mutum shida ƴan ƙasar Sifaniya.
A wani zama na ƴan difulomasiyya a Abuja, mai magana da yawun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), Peter Afunaya ya ce, an kama ƴan Poland ɗin ne a lokacin zanga-zangar da laifin ɗaga tutar wasu ƙasashe.
Sai dai, ma’aikatar harkokin ƙasashen waje na ƙasar ta musanta zargin ta wani gidan jarida (TVP world), ta na mai cewa ɗalibai shida da malaminsu ba su shiga zanga-zangar ba, amma sun ɗauki hotuna.
Jaridar ta kuma ce ɗaliban da malamin nasu sun zo gudanar da wani shiri ne a Jami’ar Bayero a ƙarƙashin karatunsu na tsangayarsu ta ‘Afrikan Studies’ daga Jami’arsu ta Warsaw a ƙasar.
Kazalika, sun bar Poland ne a ranar 1 ga watan Agusta wanda aka tsara za su dawo a farkon watan Satumba.
Daga ƙarshe, gwamnatin ƙasar Poland ta hannun Mataimakin ministan ma’aikatar, Jakob Wisniewski ta roƙi Nijeriya ta sako ƴaƴanta da aka kama.
