Gwamna Abba ya jaddada aniyarsa ta yaƙar cin hanci a Jihar Kano

Spread the love

Gwamnan Kano, Abba kabir Kabir Yusuf ya jaddada aniyarsa ta yaƙar cin hanci a faɗin Jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne a taron ƙarawa juna sani a kan cin hancin da aka yi a Dawakin Kudu ga dukkan Daraktocin jihar.

Gwamnan, wanda mataimakin shi, Com Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta ya jaddada cewa gwamnatin su ta nan tana kawo tsare-tsare da shirye-shirye da za su ci da jihar gaba.

Ya cigaba da cewa, waɗannan tsare-tsare da ake yi, zasu kawo cigaba mai ɗorewa a faɗin jihar Kano musamman ganin jami’iyyar su ta NNPP ba za ta lamunci wani nau’in cin hanci ko yaya yake ba.

Ya umarci Daraktocin su yi amfani da ilmin da za su koya domin ganin sun ci da Jihar Kano gaba.

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Rimingado ya bayyana cewa, an shirya wannan taron ne ga Daraktocin da su ke aikin gwamnati domin su san yadda za su yaƙi cin hanci a cikin ayyukan su.

Daga ƙarshe ya ja kunnen duk wanda hukama ta kama da laifin cin hanci, lallai doka za ta yi aiki a kan shi.

By ukarofi