
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban kwamitin Olympics na ƙasa-da-ƙasa (OIC), Thomas Bach ya ce zai sauka daga muƙaminsa yayin da wa’adinsa na biyu ya ƙare a shekarar 2025.
Bach wanda ɗan ƙasar Jamus ne ya faɗi hakan ne kwana ɗaya kafin ƙarƙare gasar Olympics da ke gudana a Farisa babban bankin ƙasar Faransa a wani zama na kwamitin.
Ya ce akwai buƙatar a samu sauyi a shugabancin kwamitin tare da bayar da haƙuri ga waɗanda ba su ji daɗin hukuncin nasa ba musanman cikin mambobin kwamitin da suka ɓukaci ya tsawaita zamansa a kujerar.
Bach wanda ya taɓa zama zakara a wasan tsalle na katanga (fencing) yayin Olympics na shekarar 1976, an zaɓe shi ne a 2013 a wa’adin shekaru takwas inda daga baya ya sake yin nasarar wani wa’adin shekaru huɗu a zaɓen 2021.
Za a gudanar da zaɓen sabon shugaban na OIC ne a ƙasar Girka a lokacin zama da za a yi watan Maris na shekara mai zuwa sannan a miƙa ragamar shugabancin a ranar Olympic – 23 ga watan Juni a lokacin da Bach zai sauka daga kujerar.
