
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce mafi yawancin jagororin Nijeriya kamata a ce an an garƙame ko rataye su a madadin raba mu su muƙamai.
Obasanjo ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da ƴan majalisar wakilai shida da ke jagorantar ƙudirin neman shekara shida ga kowane wa’adi.
Ya ce, a yayin zaɓar shugabanni na gari sai an yi la’akari da halayyarsu, ya na mai cewa Nijeriya ta na tsaka mai wuya da sai ta ɗauki matakan da su ka dace wajen ƙalubale da yawa da ke fuskantar ta.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce “babbar damuwarmu ita ce kanmu. Har sai mun kula da kawunanmu. Matuƙar za a samu wa’adin shekaru huɗu, shida ko ma bakwai, sannan kuma mutanen sune waɗanda ke nan da irin tunaninsu da kuma tsarin da aka saba, to ba za ta canza ba.”
Ya ƙara da cewa, duk da cewa tsarin demokraɗiyya ake yi a Nijeriya, akwai buƙatar a yi nazari akan ta da kuma tsarin gwamnatin da kuma halayyar masu mulki.
“Tare da girmamawa, ya kamata a garƙame da dama daga cikin su, a rataye wasu. Wannan ita ce gaskiyar magana”, inji shi.
Ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya kan irin yadda su ke zaɓar shugabanni, ya na mai cewa a ke duba halayen waɗanda ake zaɓa da kuma tarihinsu.
