Akwai layin waya miliyan 30 da ba a haɗa su da NIN ba, inji kamfanonin sadarwa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban ƙungiyar Masu Gudanar da Harkokin Sadarwa ta Nijeriya, Gbenga Adebayo, ya bayyana cewa sama da layukan waya miliyan 30 ba su haɗu da lambar katin shaidar ɗan ƙasa yadda ya kamata ba, kuma suna cigaba da fuskantar haɗarin kullewa.

Ya ce, waɗannan layukan sun fi yawa a cikin na’urorin bin diddigin motoci, na’urorin MiFi, na’urorin WiFi, da kuma injunan tallace-tallace.

“Muna duba yiwuwar sama da katunan SIM miliyan 30, gami da waɗanda ke cikin na’urorin dijital daban-daban, waɗanda ba a haɗa su da NIN daidai ba. Yawancin waɗannan sim ɗin suna cikin na’urorin gano motoci, injinan POS, MiFi, WiFi, da sauran na’urori da dama da ke amfani da SIM wajen aiki,”

Adebayo ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Alhamis.

Wannan lamarin ya zo ne a bayan ruɗanin baya-bayan nan da aka samu sakamakon toshe layukan da ba a haɗa su da lambar NIN ba.

A ƙarshen makon da ya gabata, kamfanonin saarwa sun fara hana layukan waya da ba a haɗa su da NIN ba aiki, kwanaki kafin wa’adin Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta 31 ga Yuli, 2024.

Tun daga watan Fabrairun 2024, kamfanonin sadarwa sun aiwatar da aikin yanke layuka waya bisa ga umarnin NCC. A ƙarshen 2023, mai gudanarwa ya nemi kamfanonin da su buɗe layukan ba a samu nasarar haɗa su da NIN a cikin matakai uku ba, inda zai ƙare Yuli 31, 2024.

Masana masana’antu sun shaida cewa tun da farko an kulle layukan waya miliyan uku kafin hukumar sadarwar Nijeriya ta umurci kamfanonin da su buɗe layukan wayar da aka kulld.

A cewar Adebayo, an katse waɗannan masu amfani da layin ne saboda saɓani a cikin bayanan da ke akwai tsakanin kamfanonin sadarwa da kuma hukumar kula da sa ido ta ƙasa.

“Akwai lokutan da mutane suka ba da NIN, amma bayanin bai yi daidai da bayananmu ba,” inji Adebayo.

“Dole ne a warware waɗannan bambance-bambance a cibiyoyin ayyuka don tabbatar da ingantaccen aiki.”

Yayin da lokacin da aka yanke ya zo daidai da zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar, Adebayo ya jaddada cewa babu wata alaƙa da wannan, domin matakin ya faro tun kafin zanga-zangar.

By ukarofi